Dangote Ya Ƙara Yawan Man Fetur Da Matatarsa Ke Tacewa A Rana
Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga 700,000 a rana, bayan wani gwajin da hukumomin da ke kula da harkokin matatun mai suka gudanar. Sabon adadin ya nuna cewa matatar ta ƙara ƙarfin aikinta daga ganga 650,000 zuwa 700,000 a kowace rana, lamarin da ke ƙara kusantar da ita ga burinta na zama ɗaya daga cikin manyan matatun mai a duniya. Mataimakin shugaban sashen mai da iskar gas na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya ce wannan ci gaban na cikin shirye-shiryen faɗaɗa ayyukan matatar domin ninka yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga miliyan 1.4 a r
