Yadda aka kama mutumin da ya nemi shawarar ChatGPT don kashe ɗansa
GARGADI GAME DA ABUBUWAN DA KE CIKI: Wannan rahoton ya na ɗauke da bayanai masu tayar da hankali da suka shafi kashe kai."Na bayar da kyautar 50,000 ...
Ammasco Radio90.7 FM · Gaskiya Tushen NasaraAMMASCO RADIO NEWSROOM
GARGADI GAME DA ABUBUWAN DA KE CIKI: Wannan rahoton ya na ɗauke da bayanai masu tayar da hankali da suka shafi kashe kai."Na bayar da kyautar 50,000 ...
Gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da kisan wasu ’yan Najeriya biyu da aka yi a Afirka ta Kudu, tare da neman gudanar da bincike cikin gaggawa kan musabbabin mutuwarsu. Mai magana da yawun ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Oluwafemi Adeniyi, ya ce lamarin ya ƙara jefa shakku kan tsaron baƙi a Afirka ta Kudu, musamman ’yan Afirka, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ƙyamar baƙi a ƙasar. Ya ce zargin hannu ko sakaci daga jami’an tsaro a mutuwar ‘yan Najeriya na ƙara dagula dangantakar da tuni ta yi tsami tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu. Gwamnatin Najeriya ta buƙaci hukumomin
Ga mazauna yankunan da ke kusa da Kogin Hadejia da sauran wuraren da ruwa ke taruwa a Jihar Jigawa, damina lokaci ne da ke haɗa fata da fargaba . Ruwan sama na kawo albarka, domin yana cika koguna da tafkuna, yana samar da ruwa ga dabbobi, yana taimaka wa manoma wajen noma, sannan ya zama hanyar samun abinci da kuɗin shiga ga dubban iyalai. Masunta na dogaro da koguna da tafkuna wajen gudanar da sana’arsu, yayin da masu kiwo ke samun ruwa da ciyawar da dabbobinsu ke buƙata. Sai dai a gefe guda, damina na zuwa da wata babbar fargaba — ambaliya . Wannan fargabar ta sake kunno kai bayan hukumomin
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da kwato kwayoyi daban-daban 5,916 da tubalan tabar wiwi guda biyar . Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Shiisu Lawan Adam , ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, a madadin Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Tijjani Murtala . A cewar sanarwar, an gudanar da samamen ne bisa sahihan bayanan sirri a yankunan rundunonin ’yan sanda na Kazaure, Gumel, Miga, Dutse, Sundumina, Taura, Babura, Ringim, Sara da Aujara . Rundunar ta ce daga cikin abubuwan da jami’
Gwamnatin Jigawa ta amince da ware Naira biliyan 12.68 domin gina sababbin gine-gine, samar da kayan aiki da gyara wasu makarantun sakandare sama da 50 a faɗin jihar. A cewar gwamnatin jihar, aikin zai shafi makarantun sakandare da ke sassa daban-daban na Jigawa, kuma an tsara shi ne domin magance ƙarancin kayayyakin more rayuwa a makarantu tare da inganta yanayin karatu ga ɗalibai da aikin koyarwa ga malamai. Ayyukan sun haɗa da gina sababbin gine-ginen makarantu, samar da kayan aiki da gyaran wasu gine-ginen da ake da su. Gwamnatin ta ce zuba jarin zai taimaka wajen rage cunkoso da matsin la
Wani jigo a jam’iyyar ADC, Dino Melaye, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da mukarrabansa da su fara tattara kayansu daga Fadar Shugaban Ƙasa. Ya na mai bayyana cewa ADC za ta doke jam’iyyar APC mai mulki a babban zaɓen shekarar 2027. Melaye ya ce sakamakon zaɓen zai Kara fito da rashin gamsuwar ’yan Najeriya da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wadda ya zarga da gaza magance matsalolin yunwa, rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar. Dino malaye ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi kafar Arise TV a ranar Litinin. Malaye ya jaddada kwarin gwiwa kan damar ADC na sam
An gano gawar wani Dan acaba mai suna Nura Yusuf, Wanda akai zargin ya bata makonni da suka gabata a wani kango bayan ya dauki wasu fasinja zuwa hanyar Gas Pipeline a Unguwar Sabo-Tasha, a kan hanyar Abaji-Gwagwalada da ke Babban Birnin Tarayya Abuja Rahotanni sun nuna cewa marigayin, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bagwai ta Jihar Kano, ya ɗauki wasu fasinjoji da suke nufin yankin Gas Pipeline, inda ake zargin an shake shi. Wani abokin marigayin na kud da kud, Ibrahim Baba, wanda ya tabbatar wa wakilinmu da lamarin a ranar Litinin, ya ce an gano gawar Dan acabar har ta fara ruɓewa a cikin wani kan
Dan takarar Gwamnan Jihar Kano karkashin jami'ar PDP a zaben 2027 Amb. Muhammad Bello Dalha, ya Kara da cewa, babu wani Abu A Gwamnatin APCn Kano da zai bashi tsoro Domin Gwamna ya kwabsa. Amb. Dalha yayi wadannan kalamai ne yayin hira da kafar Ammascoradio. "Kana ganin akwai wanda zai zabi Gwamna abba? Bayan Barnar da ya yi mana a filin Idi da Haj camp da Daula, haryanzu Gwamnatin Kano na biyin kudin daula idan Baka sani ba" inji Amb. Amb. Muhammad Bello Dalha ya bayyana cewa, Ilimi da inganta harkar kiwon Lafiya da bunkasa kasuwanci sune manyan abubuwan da gwamnatinsa zata sanya a gaba. Yana
Sanata Saliu Mustapha , mai wakiltar mazabar Kwara ta Tsakiya, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC , yayin da rikicin cikin gida na jam’iyyar ke ƙara tsananta gabanin zaɓen 2027. Mustapha ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki, magoya baya da kuma al’ummar mazabarsa. Ya ce ya fice ne saboda ganin cewa tafarkin jam’iyyar ba ya ƙara dacewa da manufofinsa da burin mutanen da yake wakilta. Sanatan ya gode wa shugabannin APC, musamman Shugaba Bola Ahmed Tinubu , bisa damar da ya samu a lokacin da yake cikin jam’iyyar, yana mai cewa ficewarsa ba zai rage j
Alkaliyar babbar kotun Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin sakin fursunoni bakwai bisa dalilan rashin lafiya, bayan ta duba shari’o’in mutane 82 da ke tsare suna jiran shari’a. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya, reshen Kano, Musbahu Nassarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a. Sanarwar ta ce an gudanar da aikin duba shari’o’in a gidajen gyaran hali na Kurmawa da Goron Dutse, a wani mataki na hanzarta gudanar da shari’a da kuma kare haƙƙin mutanen da ke tsare. Sanarwar ta ce Mai Shari’a Abdu Aboki ta duba
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ayyana Juma’a, 14 ga Agustan 2026 , a matsayin ranar hutun aiki ga ma’aikatan gwamnati a faɗin jihar, gabanin zaɓen gwamna da za a gudanar ranar Asabar. Shugaban Ma’aikatan Jihar, Elder Ayanleye Aina, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba. A cewar sanarwar, an ɗauki matakin ne domin bai wa ma’aikatan da ke buƙatar yin tafiya damar komawa yankunansu, tare da ba su damar shirya yadda za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen. Sai dai, ma’aikatan da ke gudanar da ayyukan gaggawa da mu
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta ta tallafa wa Shirin Food for Progress na Ma’aikatar Aikin Gona ta Amurka (USDA) a Najeriya, tana mai bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen ƙarfafa sarkar darajar kamun kifi da kiwon kifaye a ƙasar. Sakatariyar dindindin ta Ma’aikatar Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku ta Tarayya, Fatima Sugra Mahmood , ta bayyana hakan ne yayin da ta karɓi wata tawaga daga Partners of the Americas , wadda ke aiwatar da shirin a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Gustavo Galdo, a Abuja. A cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hul
Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah , ya yaba wa jami’an leƙen asiri da hukumomin tsaro bisa kama wasu mutane uku da ake zargi mambobin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane ce, wadda ake zargi da kai harin ranar 2 ga Agusta, 2026 a Cocin Katolika na St. Joseph da ke Inoyi-Affa , a ƙaramar hukumar Udi ta jihar. An gudanar da samamen ne ta haɗin gwiwar Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Sojojin Najeriya, ’Yan Sanda, Enugu State Forest Guard da sauran jami’an tsaro. A yayin arangamar da aka yi da waɗanda ake zargin masu garkuwar, an kashe wani daga cikin mambobin ƙungiyar, yayin da jami’an tsaron suka
Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Najeriya (NPC), tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa, ta ƙara faɗaɗa ƙoƙarin tabbatar da cewa kowane yaro a Najeriya yana da cikakkiyar shaidar kasancewa a gaban doka, ta hanyar kai ayyukan rajistar haihuwa kai tsaye zuwa asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya. An gudanar da shirin ne a Babban Asibitin Wuse da ke Abuja , a matsayin wani ɓangare na ayyukan tunawa da Ranar Rajistar Jama’a da Muhimman Bayanai ta Afirka (Africa Civil Registration and Vital Statistics Day – CRVS Day) ta 2026 . Manufar shirin ita ce sauƙaƙa wa iyaye da masu kula da jarira
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United FC ta sanar da rasuwar ɗan wasanta, Ozoh Chinedu, wanda ya rasu a lokacin wani wasan sada zumunta na share fage a ranar Talata. Ozoh yana cikin ‘yan wasan Katsina United da suka buga wasan sada zumunta da Niger Tornadoes FC a ranar Talata, a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina. Ozoh ya koma Katsina United FC ne bayan ya bar wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa da ke Arewacin Najeriya, wato Kano Pillars FC. Hukumar yaɗa labarai ta ƙungiyar Katsina United ce ta bayyana rasuwar ɗan wasan a cikin wata sanarwa mai taken “Labari mai ɗaga hankali: Ɗan wasan Katsi
Rundunar Operation HADIN KAI ta sanar da samun wani gagarumin ci gaba a yaƙin da take yi da ƙungiyar ISWAP/ISIS , bayan jerin hare-haren da ta kai kan sansanonin ƴan ta'addan a yankin Tafkin Chadi da ke Arewacin Jihar Borno. A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Jami'in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni , ya fitar, ya ce dakarun sun ƙwato wasu muhimman na'urorin sadarwa da bayanan sirri, ciki har da kyamarar bidiyo (camcorder) da ƴan ISWAP ke amfani da ita wajen ɗaukar bidiyoyin farfaganda da kuma rubuce-rubucen ayyukansu. Sanarwar ta ce binciken ƙwararru da aka gudanar kan waɗanna
Ƙungiyar Makinde Reset Nigeria Volunteers and Reset Agents ta sanar da fara rajistar masu sa kai a faɗin ƙasar domin tallafa wa burin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde , na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin haɗakar jam'iyyun APM/PDP . A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a Abuja, ta ce an buɗe rajistar ne tun daga ranar Litinin, kuma ta samu karɓuwa daga masu sha'awa a jihohi 36 na Najeriya, Babban Birnin Tarayya (FCT) da kuma 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje. Ƙungiyar ta bayyana cewa shirin na da nufin gina wata babbar cibiyar masu sa kai a faɗin ƙasar domin
Dakarun Runduna ta 4 ta Sojojin Najeriya sun yi nasarar kuɓutar da fararen hula 14 daga hannun masu garkuwa da mutane bayan wani samame da suka kai a yankunan da ke kusa da babbar hanyar Lagos–Benin a jihar Edo. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Kyaftin Kennedy Anyanwu , ya fitar, ya ce dakarun sun gudanar da aikin ne ƙarƙashin samamen Operation WABAIZIGAN , kwana guda bayan harin da masu garkuwa suka kai kan matafiya a babbar hanyar. Sanarwar ta ce sojojin sun kai samamen ne a hanyoyi da dazukan ƙaramar hukumar Ovia North East da ke jihar Edo, bayan samun sahihan bayanan sirri da misa
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin tawaga daga Ministry of Finance Incorporated (MOFI) da kamfanin Mota-Engil Nigeria gabanin bikin ƙaddamar da aikin gina Layin Dogon Jirgin Ƙasa na Kano (Kano Light Rail Project) , wanda Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da aiwatar da shi. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa , ya fitar a ranar Alhamis. Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Dr. Armstrong Ume Takang na MOFI da Shugaban Kamfanin Mota-Engil Nigeria, Mista Kola Karim , ta gana da Gwamna Yusuf a Masaukin
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na gudanar da ayyukanta cikin adalci tare da bin tanade-tanaden doka, yana mai musanta zarge-zargen nuna son kai da ake yi wa hukumar. Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya karɓi shugabannin Ƙungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) ƙarƙashin jagorancin Archbishop Matthew Ndagoso a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. A cewarsa, INEC ba ta nuna son kai ko tsoratar da kowa wajen gudanar da zaɓe. Ya ƙara da cewa korafe-korafen da jam'iyyun adawa ke yi na iya kasancewa sakamakon gazawarsu waje