AMMASCO RADIO NEWSROOM

general

Tinubu Ya Amince Da Naɗin Sabbin Shugabanni Da Mambobi A Hukumomin Tarayya

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin sabbin shugabanni da mambobi 26 a hukumomi da kwamitocin gwamnatin tarayya guda 10. Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, wanda zai jagoranci Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA). Haka kuma, Manjo Janar Junaid Bindawa ya zama shugaban Hukumar Albashi da Tsarin Albashin Ma'aikatan Ƙasa. Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Dr. Abuh Mohammed a matsayin Darakta Janar na Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Dr. Akinola Odeyemi a matsayin shugaban Kamfanin Ciniki da Wutar Lantarki na Najeriya (NBET), da kuma Dr. A

Majalisar Dokokin Faransa ta amince da ƙudirin taimaka wa wasu marasa lafiya su kawo ƙarshen rayuwarsu

Majalisar Dokokin Faransa ta amince da wani ƙudiri da zai ba da damar taimaka wa wasu marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali su kawo ƙarshen rayuwarsu, amma ƙarƙashin tsauraran sharuɗɗan doka. Batun ya shafe shekaru yana jawo muhawara a ƙasar, inda a baya Majalisar Dattawa ta yi watsi da irin wannan ƙudiri sau da dama. Idan ƙudirin ya zama doka, zai shafi manyan mutane da ke fama da cututtuka masu tsanani kuma marasa magani, waɗanda suka kai matakin ƙarshe ko kuma suke fuskantar matsananciyar azaba da magunguna ba sa iya rage musu raɗaɗi. Ƙudirin ya tanadi cewa mara lafiyar ne zai sha magani

Masana sun yi nazari kan tasirin tikitin Muslim-Muslim ga siyasar Najeriya

Bayan da jam'iyyar APC ta sake tsayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a matsayin 'yan takararta na shugaban ƙasa da mataimakinsa a zaɓen 2027 , masana harkokin siyasa sun yi nazari kan tasirin ci gaba da amfani da tikitin Muslim-Muslim . Matakin ya kawo ƙarshen jita-jitar da ta yi ta yawo cewa mai yiwuwa Shugaba Tinubu ya sauya mataimakinsa saboda matsin lamba daga wasu ƙungiyoyi da suka yi kira da a samar da daidaito tsakanin addinai a tikitin shugaban ƙasa. Masana sun bayyana cewa batutuwan addini da yanki na ci gaba da kasancewa muhimman abubuwa a siyasar Najeriya, musamman

Andy Burnham Ya Nemi Afuwa Kan Martanin Jam'iyyar Labour Game Da Rikicin Gaza

Andy Burnham, wanda ake ganin na daga cikin fitattun 'yan siyasar da ka iya jagorantar Jam'iyyar Labour a nan gaba, ya nemi afuwa kan yadda jam'iyyarsa ta fara mayar da martani game da matakan da Isra'ila ta ɗauka a Zirin Gaza. A cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Burnham ya amince cewa jam'iyyar Labour ta yi kuskure a yadda ta fara tunkarar rikicin. A farkon rikicin, Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya fuskanci suka bayan ya bayyana cewa Isra'ila na da "haƙƙin" katse samar da ruwa da makamashi zuwa Gaza. Sai dai daga baya Starmer ya fayyace cewa abin da yake n

Trump: Netanyahu Ya San Wane Ne Jagora a Tsakaninmu

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya san wane ne jagora a tsakaninsu, yana mai jaddada cewa dangantakar da ke tsakanin shugabannin biyu tana nan daram duk da rahotannin da ke cewa akwai saɓani a kan wasu batutuwa. Trump ya bayyana hakan ne a wata gajeriyar hira da ya yi da kafar Axios, inda ya ce suna da kyakkyawar alaƙa, kuma Netanyahu ya fahimci matsayin jagoranci da ke tsakaninsu. Kalaman shugaban Amurkan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran Netanyahu zai kai ziyara Fadar White House a cikin kwanaki masu zuwa. Idan ziyarar ta tabb

Nagelsmann ya sauka daga aikin horar da tawagar Jamus

Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Jamus, Julian Nagelsmann, ya sauka daga muƙaminsa bayan ficewar ƙasar daga Gasar Kofin Duniya a zagaye na biyu, kamar yadda jaridar Bild ta ruwaito a ranar Juma'a. Rahoton ya ce Nagelsmann mai shekaru 38 ya amince da barin aikinsa ne bayan tattaunawa da manyan jami'an Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Jamus (DFB). A cewar Bild , wacce ta ambato majiyoyinta ba tare da bayyana sunayensu ba, kocin ya yanke shawarar yin murabus ne bayan wani taron sirri da ya ɗauki kusan sa'o'i uku a hedikwatar DFB da ke Frankfurt a ranar Alhamis. Har zuwa lokacin wallafa rahoton, DFB ba ta fit

Rikicin Liman da Kwamitin Gudanarwa Ya Jawo Rufe Masallaci a Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe Masallacin Ibadurrahman da ke unguwar Shingen Abba a cikin garin Bauchi, sakamakon rikicin da ya daɗe yana ci gaba tsakanin limamin masallacin da kwamitin gudanarwarsa. An ɗauki matakin ne domin dakile yiwuwar ɓarkewar rikici da ka iya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a tsakanin al’ummar yankin. Kwamishinan Hisba na Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi, Barrista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne bisa umarnin kotu da kuma la’akari da yanayin rikicin da ya shafe kusan shekaru uku yana gud

Hezbollah da Isra’ila Sun Amince da Tsagaita Wuta Bayan Mummunan Artabu

Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah sun amince da tsagaita wuta bayan kwana ɗaya na kazamin faɗa da ya haddasa asarar rayuka da jikkata mutane da dama a Lebanon. Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar, yayin da kakakin rundunar sojin Isra’ila ya bayyana cewa sojojin ƙasar za su ci gaba da kasancewa cikin shiri idan har bukatar komawa fagen daga ta taso. Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa cewa ci gaba da rikicin a Lebanon na iya kawo cikas ga ƙoƙarin diflomasiyya da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙoƙarin tabbatarwa tsakanin

Ba zamu sake duba sakamakon zaben fidda gwani ba, duk da korafe -korafen da ake - APC

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba za ta sake duba sakamakon zabukan fidda gwani da ta gudanar ba, duk da korafe-korafe da bukatun sake zabe daga wasu ‘yan takara da suka fadi. Jam’iyyar ta ce an kammala dukkan matakan sauraron daukaka kara kuma ana shirye-shiryen tura sunayen wadanda suka yi nasara zuwa INEC. Wani babban jami’in APC ya ce mafi yawan korafe-korafen da aka shigar ba su da karfi, yayin da rahotannin kwamitocin daukaka kara ba su kawo wani babban sauyi ga sakamakon da aka sanar ba. Ya kara da cewa kasa da kashi biyu cikin dari na korafe-korafen ne suka samu nasara. Sai dai wasu dag

Majalisar Dattawa ta bayar da umarnin kamo tsohon shugaban NNPCL

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da bibiyar kashe kuɗaɗen al’umma ya buƙaci hukumomin tsaro su kamo tsohon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, Mele Kyari, bisa zargin yin kunnen uwar shegu da gayyatar da kwamitin ya yi masa. Kwamitin ya gayyaci Kyari ne domin ya yi bayani kan wasu tambayoyi da suka shafi binciken kuɗaɗe kusan naira tiriliyan 210, waɗanda kwamitin ya ce har yanzu bai gamsu da bayanin yadda aka sarrafa su ba a lokacin da yake shugabantar kamfanin tsakanin shekarun 2017 zuwa 2023. Tun da farko, ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya ne ya fara nuna damuwa kan waɗan

Hezbollah ta harba makamai masu linzami kan sojojin Isra’ila a kudancin Lebanon

Ƙungiyar Hezbollah ta bayyana cewa ta harba jerin makamai masu linzami kan tarin motocin sojin Isra’ila tare da dakarunsu da ke kudancin Lebanon da safiyar yau. A cikin wani saƙo da ta wallafa a manhajar Telegram, ƙungiyar ta ce ta kai farmakin ne kan wani taron sojojin Isra’ila a wajen garin Beit Yahoun da ke kudancin ƙasar. Hezbollah ta bayyana harin a matsayin martani ga abin da ta kira karya yarjejeniyar tsagaita wuta, tare da ci gaba da hare-haren da Isra’ila ke kai wa kan ƙauyukan kudancin Lebanon. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Isra’ila ba ta fitar da wani bayani ba

ICPC Ta Yi Watsi Da Buƙatar El-Rufai Ta Samun Kulawar Asibiti

Mai bai wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya zargi Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) da hana El-Rufai samun kulawar lafiya yayin da yake tsare a hannunta. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Adekeye ya ce El-Rufai ya koka kan matsalar ƙaiƙayi da kumburi a idanunsa, lamarin da ya sa ya nemi a kai shi asibiti domin a duba lafiyarsa. Sai dai, a cewarsa, jami’an ICPC ba su amince da wannan buƙata ba. Adekeye ya bayyana cewa an kai El-Rufai wani asibitin ido a ranar 4 ga watan Yuni, amma daga bisani matsalar ida

Najeriya Ta Shirya Kwaso Ƴan Ƙasarta 1,000 Daga Afirka Ta Kudu Sakamakon Zargin Nuna Wariya

Gwamnatin Najeriya ta fara shirye-shiryen kwaso sama da ƴan ƙasarta 1,000 daga Afirka ta Kudu sakamakon ƙara yawaitar tashin-tashina da zargin nuna adawa ga baƙi a ƙasar. Matakin ya biyo bayan yadda Ghana ta fara dawo da wasu daga cikin ƴan ƙasarta bayan barazanar da zanga-zangar adawa da baƙi ta haifar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya ce an fara tantance ƴan Najeriya da suka nuna sha’awar komawa gida tun ranar Alhamis. “Muna sa ran fara kwashe kusan mutum 1,000, duk da cewa har yanzu ba mu da tabbataccen adadin waɗanda za a dawo da su,” in ji Ebienfa. Ya kuma c

Babbar Kotun Tarayya ta ɗage sauraron shari’ar da Nafiu Bala Gombe ya shigar kan shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark zuwa ranar 8 ga Yunin da muke ciki

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron shari’ar da Nafiu Bala Gombe ya shigar kan shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark zuwa ranar 8 ga Yunin da muke ciki . Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa Mai Shari’a Peter Lifu ne ya ɗage shari’ar bayan lauyan Gombe, Robert Emukpoeruo (SAN), ya nemi ƙarin lokaci saboda rashin halartar lauyoyin wasu ɓangarorin da ke neman a haɗa su cikin shari’ar. Yayin zaman kotun, lauyan ADC, Shaibu Aruwa (SAN), ya tunatar da kotun cewa tsohon mai sauraron ƙarar, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya riga ya yi la’akari da waɗannan ɓ

Wike ya danganta kiwon shanu a Abuja da matsalolin tsaro

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana kiwon shanu barkatai a cikin birnin Abuja a matsayin batu da ya shafi tsaron ƙasa, yana mai cewa matsalar na buƙatar tattaunawa ta gaskiya da kuma samar da mafita mai ɗorewa. Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kai-tsaye da manema labarai a ranar Litinin, inda ya nuna damuwa kan yadda ake ganin shanu suna kiwo a gefen tituna da kuma sabbin wuraren da aka bunƙasa a babban birnin ƙasar. “Wannan batun tsaron ƙasa ne. Dole ne mu fuskanci gaskiya,” in ji ministan, yana mai cewa yunkurin magance matsalar kan fuskanci suka daga

Atiku Abubakar ya Zama Dan takarar shugaban kasa a Jam'iyar hamayya ta ADC

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC domin babban zaɓen shekarar 2027. An sanar da sakamakon zaben ne a daren Laraba cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na jam’iyyar, inda aka bayyana cewa Atiku ya doke tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kuma tsohon ma’aikacin banki, Mohammed Hayatu-Deen a takarar. Atiku ya kayar da Amaechi da Hayatudeen domin samun tikitin takarar shugaban ƙasa na ADC. Sakamakon ƙarshe ya nuna cewa, Atiku Abubakar ya sami kuri’u 1,855,787 inda Amaechi ya samu kuri’u 509,397 sai kuma Hayatudeen

Tinubu ya bayar da wannan umarni ne cikin saƙonsa na bikin Ranar Yara ta shekarar 2026 wato yau Laraba

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da ma’aikatun da abin ya shafa da su ƙara ƙaimi wajen kare makarantu da ke yankunan da ake fuskantar barazanar tsaro a faɗin ƙasar nan. Tinubu ya bayar da wannan umarni ne cikin saƙonsa na bikin Ranar Yara ta shekarar 2026 wato yau Laraba, kamar yadda jaridar PUNCH Online ta ruwaito. Shugaba Tinubu ya ce gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen Samar da wani tsari na musamman na ceto yara da sauran al’umma masu rauni da aka yi garkuwa da su, musamman waɗanda aka sace a jihohin Oyo da Borno kwanan nan. “A yayin da muke bikin wannan rana ta musamman, wa

Kashim Shettima ya roki Yan Najeriya da su cigaba da hakuri da gwamnatin Shugaba Tinubu

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya sake jaddada kudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na rage wa ‘yan Najeriya radadin matsin tattalin arzikin da suke fuskanta. Shettima ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan gudanar da sallar Eid-el-Kabir a filin Idi na Ramat Square da ke Maidugurin Jihar Brono Mataimakin Shugaban Kasar, wanda ya bayyana cewa tsadar rayuwa ta karu a duniya baki daya, ya roki ‘yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati.

EFCC ta mika sale Mamman gidan gyaran Hali na kuje dake Abuja

Hukumar EFFC Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya ta mika tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, zuwa Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke Abuja domin fara zaman hukuncin daurin shekaru 75 da kotu ta yanke masa. Hakan ya biyo bayan umarnin da Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, ya bayar a ranar Talata, bayan gabatar da Mamman a gaban kotun da EFCC ta yi. DCL Hausa ta ruwaito cewa kotun ta kuma saurari bukatar EFCC na kwace wasu karin kadarori guda biyar da ake zargin suna da alaka da Mamman, ciki har da gidaje da otel-otel da ke Abuja da Kaduna.

Tinubu ya gana da wasu gwamnoni a Legas bayan nasarar da ya yi a zaɓen fidda gwani

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, a gidansa da ke Ikoyi a jihar Legas bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC. Jaridar Punch ta rawaito cewa Anyim, wanda shi ne shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya kai ziyarar ne kwanaki biyu bayan bayyana Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027. Kazalika Tinubu ya kuma gana da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, da kuma gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu.