Majalisar Dokokin Kano Ta Bukaci Gwamnatin Jiha Ta Samar da Cibiyoyin Koyon Sana’o’i a Duk Ƙananan Hukumomi 44
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci Gwamnatin Jihar da ta samar da cibiyoyin koyon ƙananan sana’o’i a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin inganta koyon sana’o’i da ƙarfafa matasa su dogara da kansu. Wannan ya biyo bayan ƙudirin da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ungogo, Sa’ad Aminu Sa’ad , ya gabatar a zaman majalisar na ranar Litinin. A cikin ƙudirin, ya buƙaci gwamnati ta kafa cibiyoyin koyon sana’o’i a yankunan Tudun Fulani da Zango da ke ƙaramar hukumar Ungogo. Sai dai bayan tattaunawar da aka gudanar kan ƙudirin, majalisar ta ga ya dace a faɗaɗa shirin domin ya shafi dukkan ƙan
