Me ya sa wasu ƴan Kannywood ke fita daga ƙungiyar Triple R mai tallata Tinubu?
Wasu fitattun jaruman Kannywood na ci gaba da sanar da ficewarsu daga ƙungiyar Triple R Kannywood for Renewed Hope , wadda aka kafa domin tallata manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Na baya-bayan nan da ya sanar da ficewarsa shi ne fitaccen jarumi Rabiu Rikadawa , wanda ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya bayyana a matsayin rashin tabbas da kuma rashin bin dokoki da ƙa'idojin ƙungiyar . A cewar Rikadawa, yadda ake tafiyar da harkokin ƙungiyar bai dace da abin da aka kafa ta a kai ba, lamarin da ya sa ya yanke shawarar ficewa. Kafin s
