AMMASCO RADIO NEWSROOM

local

Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 27 a Sabbin Hare-Hare

Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da cewa ta samu gagarumar nasara a wasu hare-haren da ta kai a sassa daban-daban na ƙasar, inda ta kashe ’yan ta’adda 27 tare da kama mutane 10 da ake zargi da aikata laifuka. Rundunar ta kuma bayyana cewa sojojinta sun yi nasarar ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su cikin sa’o’i 48 da suka gabata. A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, an gudanar da hare-haren ne cikin haɗin gwiwa tsakanin sojojin ƙasa da na sama a jihohin Borno da Plateau da Nasarawa da Akwa Ibom , da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) , bayan samun sahihan bayanan sirri. Sanarwar ta ce

Ibrahim Adam Ya Samu Sabon Muƙami a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nada Ibrahim Adam a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai (Special Adviser on Information), a wani yunƙuri na ƙara bai wa matasa damar shiga harkokin mulki tare da inganta isar da ayyukan gwamnati ga al’umma. Mai magana da yawun gwamnan, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Ibrahim Adam, mai shekaru 32 a duniya, ya kammala karatun Digiri a fannin Kimiyyar Siyasa (Political Science) daga Jami’ar Bayero Kano (BUK). Ya shahara a matsayin ɗaya daga cikin matasan masu tasiri a

Gwamnatin Kano ta Kudiri aniyar rage talauci ta hanyar amfani da sabbin hanyoyin tallafawa al'umma

Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da aniyarta na rage talauci ta hanyar aiwatar da shirye-shirye da manufofin da za su inganta rayuwar al’umma. Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa na jihohin Arewa maso Yamma kan hanyoyin rage talauci, wanda UNICEF da Tarayyar Turai suka shirya. Ya ce talauci na ci gaba da zama babban ƙalubale a yankin, inda yake shafar miliyoyin mutane ta fannin ilimi, kiwon lafiya, abinci mai gina jiki da damar samun abin yi. Ya ƙara da cewa magance matsalar na buƙatar haɗin kai da jajircewar gwamnati da sauran

Ƴanbindiga sun sace ɗalibai shida na Federal Polytechnic Kaura-Namoda a Zamfara

Wasu da ake zargin ƴanbindiga ne sun yi garkuwa da ɗalibai shida na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic) da ke Ƙauran-Namoda a jihar Zamfara, bayan sun kai hari gidan da ɗaliban ke zaune a wajen harabar makarantar. An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wani gida da ke gefen unguwar Low-Cost a garin Ƙauran-Namoda, inda maharan suka kutsa cikin gidan tare da yin awon gaba da daliban. Shugaban ƙaramar hukumar, Mannir Haidara Ƙaura, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban cikin ƙoshin la

Yansanda Sun Gano Maɓoyar Masu Ƙera Bindigogin Farauta a Yobe

Rundunar Ƴansandan Najeriya reshen Jihar Yobe ta sanar da gano wani haramtaccen wurin ƙera makamai a garin Potiskum, tare da kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a aikin. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana wannan nasara a matsayin ɗaya daga cikin manyan ci gaban da ta samu wajen yaƙi da laifuffuka a jihar. Kakakin rundunar a jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce kamen ya biyo bayan sabbin tsare-tsaren da Kwamishinan ƴansandan jihar ya ƙaddamar domin daƙile ayyukan ta’addanci da sauran laifuffuka a faɗin Yobe. A cewarsa, a ranar 2 ga Yunin 2026 da misalin ƙarfe shida na yamm

Kotu Ta Yanke Wa Mutum Huɗu Hukuncin Kisa Kan Harin Cocin Owo

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin hannu a harin da aka kai Cocin Katolika ta Saint Francis da ke Owo a Jihar Ondo a ranar 5 ga Yunin 2022. Mai Shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin ne bayan kotun ta same su da laifuka tara da suka haɗa da ta’addanci, haɗa baki domin aikata laifi, satar mutane da kuma kashe masu ibada sama da 40 a harin da ya girgiza Najeriya. Waɗanda aka yanke wa hukuncin na daga cikin mutum biyar da Hukumar Tsaro ta DSS ta gurfanar kan zargin hannu a harin, wanda ya kuma yi sanadin jikkatar fiye

Wasu iyaye Sun Zargi Gwamnati da yin watsi da yaran da aka sace a Borno

Gwamnatin Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan rashin kuɓutar da ɗaliban makaranta 42 da aka sace a jihar Borno, waɗanda har yanzu ke hannun ƴan bindiga. Iyayen ɗaliban sun bayyana damuwa da cewa gwamnati kamar ta yi watsi da lamarin, inda suka kwatanta yadda ake ganin ana ɗaukar matakan gaggawa a wasu jihohi kamar Oyo, yayin da nasu batun ke tafiyar hawainiya. Sai dai mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya musanta zargin, yana mai cewa gwamnati na ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin ganin an kuɓutar da yaran. Rahotanni sun nuna cewa ɗa

Amurka ta ware dala miliyan 3.5 domin sa ido kan tashe-tashen hankula masu alaka da addini a Najeriya

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da ware dala miliyan 3.5 (kimanin Naira biliyan 5 ) domin tallafawa shirye-shiryen tattara bayanai da rahotanni kan take hakkin ‘yancin addini da tashe-tashen hankula masu alaka da addini a Najeriya. Shirin, wanda Ofishin Kula da ‘Yancin Addini na Kasa da Kasa (IRF) ya sanar a ranar 22 ga Mayu, 2026, na da nufin karfafa ayyukan kungiyoyi da cibiyoyi da ke sa ido tare da rubuta bayanai kan hare-haren da suka shafi addini da akida a fadin Najeriya. A cewar sanarwar, za a gudanar da aikin na tsawon watanni 24 zuwa 48 , kuma za a bai wa wata kungiya ko huk

Abin takaici ne yadda ake rasa rayuka a Kano — Gwarzo

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NDC kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya zarge shi da yin sakaci wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar. A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Kwamared Aminu Abdussalam ya bayyana cewa yanayin tsaro a Kano ya taɓarɓare fiye da kowane lokaci a tarihin baya-bayan nan. Ya ce a wasu ƙananan hukumomi irin su Tsanyawa, Shanono da Gwarzo, an samu hare-hare da suka yi sanadin kisan mutane da kuma kwashe dukiyoyi. Ya kuma yi zargin cewa har yanzu akwai wasu da ke tsare sama da watanni shida sakam

Tsohon kakakin sojoji ya faɗa hannun ƴanbindiga a Katsina

Ana zargin wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a Jihar Katsina. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Matazu lokacin da tsohon jami'in sojan da matarsa ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Katsina. Maharan sun tare motar da suke ciki tare da yin awon gaba da su zuwa wani wuri da ba a bayyana ba. Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa direban motar ya samu raunukan harbin bindiga yayin harin, amma ya samu nasarar tserewa daga hannun maharan. Har zuwa lokacin haɗa wannan r

Gwamna Makinde ya nuna Bimbo Adekanmbi a matsayin wanda yake so ya gaje shi a Oyo

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana Bimbo Adekanmbi a matsayin wanda yake fatan zai gaje shi a kujerar gwamnan jihar a zaben shekarar 2027. Makinde ya bayyana hakan ne yayin taron gangamin haɗin gwiwa na jam’iyyun PDP da APM da aka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, inda aka kuma kaddamar da Adekanmbi a matsayin ɗan takarar gwamna na bai ɗaya na jam’iyyar APM. Gwamnan ya ce al’ummar jihar Oyo sun amfana da tsare-tsaren gwamnatinsa na “Omituntun 1.0” da “Omituntun 2.0”, yana mai bayyana cewa yanzu lokaci ya yi na aiwatar da “Omituntun 3.0”. Haka kuma, Makinde ya shawarci Adekanm

Dakta Dahir Hashim ya yaba wa Gwamna Abba kan nuna hikima a batun fitar da ƴan takarar APC

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa abin da ya bayyana a matsayin nuna kwarewa, gogewa da hikima wajen tafiyar da batun fitar da ƴan takarar jam’iyyar APC a jihar. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Dakta Dahir Hashim ya taya gwamnan murnar nasarar gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar cikin lumana a fadin jihar Kano, yana mai cewa tsarin ya gudana cikin natsuwa da fahimtar juna tsakanin masu ruwa da tsaki. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna ƙwarewar siyasa ta hanyar haɗa k

‘Aminu Abdussalam shi ne ɗan takararmu na gwamna a 2027’ — Kwankwaso

Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar NDC a zaɓen shekarar 2027. Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya kuma sanar da cewa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna zai nemi kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya. Ya ce an ɗauki matakin ne bisa la’akari da gaskiya, biyayya da ƙwarewa, waɗanda ya bayyana a matsayin ginshiƙan haɗin kai da ci gaban Kwankwasiyya. Sanarwar na zuwa ne bayan kwanaki ana gudanar da tattaunawa tsakanin mambobin Kwankwasiyya da wasu manyan ƴan siyasa kan shi

‘Mun kafa tubalin warware matsalolin Najeriya’ — Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa ta shimfiɗa tubalin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasar, duk da cewa har yanzu ba a kai ga cimma dukkan manufofin da aka sa gaba ba. A jawabinsa na cikar shekara uku a mulki, Tinubu ya bayyana cewa ya fahimci irin ƙalubale da sadaukarwar da iyalai suka fuskanta a cikin shekarun baya-bayan nan, tare da nuna ƙwarin gwiwar cewa Najeriya na kan hanyar samun ci gaba. Shugaban ya jaddada cewa harkar tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi bai wa muhimmanci, yana mai cewa ana ci gaba da samun nasarori duk da ƙalub

Gwamnati ta gargadi mazauna yankin Mokwa su fice saboda barazanar sake aukuwar ambaliya

Gwamnatin ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja ta umarci mazauna yankunan da ambaliya ta shafa a bara da su fice daga wuraren saboda barazanar sake aukuwar ambaliya. A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran shugaban ƙaramar hukumar, Haruna Saidu Kinbokun ya fitar ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu taruwar ruwa a yankin sakamakon toshewar hanyar ruwa da ake zargin aikin sake gina layin dogo ya haddasa. Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa aikin da kamfanin CPN ke yi ya kawo cikas ga hanyar ruwa na ɗan lokaci, lamarin da ya janyo kwararar ruwa mai yawa da ka iya haifar da sabon amb

Hukumar Hisbah ta kama wani mutum bisa zargin yi wa yarinya mai shekara 11 fyaɗe

Hisbah a ƙaramar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina ta kama wani mutum bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekara 11 fyaɗe a unguwar Bakin Sabuwar Kasuwa. A cewar sanarwar da jami’in sashen fasahar sadarwa na Hisbah a Dutsinma, Malam BYAREEMA ya fitar, mazauna unguwar ne suka kama wanda ake zargin tare da tsare shi kafin jami’an Hisbah suka isa wurin domin karɓarsa da fara bincike. Sanarwar ta ƙara da cewa an samu wanda ake zargin cikin maye yana riƙe da wandonsa a hannu. Hukumar Hisbah ta yaba da haɗin kan al’umma wajen taimakawa jami’an tsaro, tare da kira ga iyaye su ƙara sanya ido kan ya

Gaya ya rasa tikitin Sanatan Kano ta Kudu bayan komawarsa NDC

Tsohon Sanata Kabiru Gaya ya rasa tikitin takarar Sanatan Kano ta Kudu na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) duk da sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar gabanin zaɓen 2027. Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar ta amince da Kassim Batayya a matsayin ɗan takarar sasanci na mazabar Sanatan Kano ta Kudu a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da ke Miller Road. Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan Gaya ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa NDC yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa a jihar Kano kafin zaɓen 2027. An ruwaito

NBS: Kudin abinci mai lafiya ya kai N1,513 a kowace rana a watan Fabrairu

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin kudin cin abinci mai lafiya ga mutum guda a Najeriya ya kai N1,513 a kowace rana a watan Fabrairu. Hukumar ta bayyana hakan ne cikin rahotonta na “Cost of a Healthy Diet (CoHD)” na watan Fabrairu 2026 da aka fitar a Abuja. A cewar NBS, wannan adadi ya karu da kashi 3.76 idan aka kwatanta da N1,458 da aka samu a watan Janairu 2026. Hukumar ta bayyana cewa CoHD shi ne mafi arha hadin abinci daga cikin kayan abinci na gida da ake samu, wanda ke cika ka’idojin abinci mai gina jiki da aka amince da su a duniya. Ta ce ana amfani da wannan m

ICPC ta bayyana dalilin hana shugabannin ADC ganin El-Rufai

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaƙa (ICPC) ta kare matakin da ta dauka na hana shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, tana mai cewa matakin ya yi daidai da umarnin kotu da ke kan lamarin. Kakakin hukumar, John Odey, ne ya bayyana haka ga PUNCH Online a ranar Asabar, yayin da yake mayar da martani kan zargin da ADC ta yi na cewa an hana shugabanninta shiga kuma an nuna musu rashin mutunci yayin ziyarar da suka kai ranar Juma’a. Odey ya ce ICPC ta riga ta mayar da martani ga wasikar da ADC ta aike t

Bauchi: Aikin gwamnati ba na sayarwa ba — gwamnati ta gargadi jama’a kan tayin aiki na bogi

Gwamnatin Jihar Bauchi, ta hannun Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta Jiha (Civil Service Commission), ta gargadi jama’a da su guji karɓar tayin aikin bogi, tana mai jaddada cewa ayyukan gwamnati a jihar ba na sayarwa ba ne. Wannan gargadi ya biyo bayan cafke wani mutum mai suna Saleem Alhassan, wanda aka fi sani da “Jagaban Ningi,” da rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta yi bisa zargin forgery da wasu laifuka masu alaƙa. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai a ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na jihar Bauchi, Awwal Waziri, ya fitar a ranar Asabar. A cewar sanar