Gwamnatin Tarayya ta amince da wani shirin gaggawa na tattalin arziki na tsawon kwanaki 90, da nufin rage tsadar rayuwa da sauƙaƙa wa ’yan Najeriya wahalhalun tattalin arziki.
Wata Babbar Kotun Shari’a a Jihar Kano ta umarci rundunar ’yan sanda da ta gudanar da bincike kan zarge-zargen haɗa baki wajen aikata laifi, cin zarafi, tsoratarwa da kuma rushe dukiya ba bisa ƙa’ida ba da ake yi wa Muazu Abdullahi-Gwarzo, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Gwarzo/Kabo a Majalisar Tarayya.
Mazauna ƙauyen Birnin Tudu da ke ƙaramar hukumar Gummi a Jihar Zamfara, sun ce sun kashe sama da ’yan bindiga 30 a wani artabu da ya ɗauki tsawon kwanaki uku, bayan da wasu mahara ɗauke da makamai suka kai wa al’ummar yankin hari.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da shugabannin jam’iyyar APC, za su ƙaddamar da yaƙin neman sake zaɓensa a jihar Kaduna ranar Asabar, yayin da jam’iyyar mai mulki ke ƙara ƙaimi wajen neman goyon bayan al’umma a Arewacin ƙasar.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi bayanin yadda aka kashe kuɗaɗen da aka ware domin shirin tunkarar cutar Ebola, tare da yin tambayoyi kan lokacin da aka ɗauka kafin tabbatar da bullar cutar.
Mataimakin Firaministan Rasha, Alexander Novak, ya ce ana kammala takardun yarjejeniyar samar da man, yayin da ake sa ran ƙarin jigilar man fetur zuwa Amurka a nan gaba.
Wakilin dindindin na Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce karɓar daftarin kasafin kuɗin ya zama tarihi, yana mai cewa shi ne karo na farko cikin shekaru 66 da shugaban ƙasar ya karɓi irin wannan takarda.
Jam’iyyar APC ta ce ba ta da hannu a duk wani shiri na cutar da Atiku Abubakar, tare da kira ga Timi Frank da ya miƙa hujjojinsa ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike.
Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta yi kakkausar suka kan harin da wasu Yahudawa ’yan kama wuri zauna suka kai wa jami’an diflomasiyyar Turai da wani magajin gari na Faransa a Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.
Shugaba Bola Tinubu zai halarci gangamin yaƙin neman zaɓen sake zaɓensa a jihohi 12 na Nijeriya gabanin zaɓen 2027, yayin da shugabannin jam’iyyar APC za su wakilce shi a sauran jihohin ƙasar.
Akalla mata Musulmi 500 da suka hada da malamai, masu wa’azi da shugabannin Da’awah daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja, sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2027.
Matan sun bayyana matsayinsu ne a karkashin kungiyar Muslim Intellectuals Forum , yayin wani taron tuntuba da aka gudanar a Kaduna ranar Lahadi.
A cewarsu, sun yanke wannan shawara ne bisa la’akari da nasarorin da suka ce gwamnatin Shugaba Tinubu ta samu tun bayan hawanta kan mulki.
Sun ambaci bangarorin ilimi, tsaro, samar da ababen more rayuwa da
Jerin sunayen wanda Sakatariyar Hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, an fitar da shi ranar Asabar a Abuja wanda ya ƙunshi ’yan takara da jam’iyyun siyasa 18 suka tsayar domin neman kujerar shugaban ƙasa.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa daga cikin ’yan takarar shugaban ƙasa 18, 16 maza ne, wanda ya kai kashi 88.9 cikin 100, yayin da biyu mata ne.
NAN ta kuma ruwaito cewa maza da ke cikin jerin Yan takarar sun haɗa da Bola Tinubu na APC, Abubakar Atiku na Jam'iyar ADC, da Peter Obi na NDC.
Sauran sun haɗa da Adewole Adebayo na Social Democratic Party (SDP),
Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda ya gabatarwa majalisar dokokin jihar da daftarin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2027 , wanda ya kai Naira biliyan 828.64 a ranar talata domin amincewa. Kusan kashi 77 cikin 100 na kasafin kuɗin an ware shi ne domin ayyukan raya ƙasa. Kasafin kuɗin mi taken “Building Your Future IV” , ya ware Naira biliyan 637.91 , wato kashi 76.98 cikin 100 , domin ayyukan manyan ayyuka, yayin da aka ware Naira biliyan 190.73 , kwatankwacin kashi 23.02 cikin 100 , domin gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati. Adadin kasafin kudin ya ragu da Naira biliyan 69.23 idan aka
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta bayyana sunayen ’yan takarar kujerar gwamnan Jihar Kwara guda 12 da mataimakansu, domin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027.
Hakan ya ya baiwa Yan takarar damar fara shirye-shiryen yakin neman zabe gabanin babban zaɓen ƙasa.
INEC ta bayyana jerin sunayen ne a ofishin hukumar da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, a ranar Asabar, inda ’yan takarar suka fito daga jam’iyyun siyasa daban-daban.
Hukumar ta bayyana Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Yakubu Danladi-Salihu, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, yayin da Bello
Gwmnatin Tarraya ta ce tufka da warwarar da jagoran ‘yan adawa kuma ɗantakaran jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ke yi kan batun mayar da tallafin mai na nuna cewa siyasa kawai ne yake son yi da batun mayar da tallafin. A wata sanarwar da ya fitar jiya Laraba babban mai bai wa Shugaban Tinubu Shawara kan Watsa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce sauya maganar da Atiku ya yi sau uku cikin mako ɗaya ya nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar siyasa kawai yake yi da batun dawo da tallafin mai. Sanarwar ta ce daga farko mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya ce Atiku zai mayar da tallafi idan
Wata kungiyar magoya bayan APC da ke yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ta yi barazanar janye goyon bayan da take ba shi bisa radin kanta, idan har tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Kungiyar mai suna Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027, ta bayyana wannan gargadi ne cikin wata takardar korafi mai dauke da kwanan watan 25 ga Agusta, 2026, wadda ta aika wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, tare da kwafin takardar zuwa fadar shugaban kasa.
Kungiyar t
Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT), CP Ahmed Mohammed Sanusi, ya gargadi Jami’an ’Yan Sanda Masu Kula da Rukunan ’Yan Sanda (DPOs) da kada su tsare waɗanda ake zargi na tsawon fiye da sa’o’i 24 ba tare da ingantaccen umarnin kotu ko wata sahihiyar izini ta doka ba.
Sanusi ya bayar da wannan umarni ne a yayin wata ziyarar sa ido da ya kai ga Rukunin Yankunan Metro da Life Camp, inda ya duba ayyukan gudanar da aiki tare da tantance yadda jami’an ke gudanar da ayyukansu da kuma irin rawar da suke takawa.
Musamman, ya gargadi jami’an da ke sassan ’yan sandan birnin Abuja kan tsare
Tsohon Gwamnan Jihar Gombe kuma Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya bayyana cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar mutane da kuma yin shawarwari kan makomarsa ta siyasa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugabannin siyasa daga jam’iyyun PDP da ADC suna kokarin jawo Sanata Goje zuwa jam’iyyunsu, tare da matsa masa lamba ya sauya sheka, bayan da ya bayyana cewa APC ba za ta ba shi tikitin takara ba.
Da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a gidansa da ke Gombe ranar Asabar, Goje ya musanta cewa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyyar siyasa, inda ya tabbatar da cewa
Tsohon Gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Rabiu Kwankwaso , ya jajanta wa iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwale da ya afku a Gorau, ƙaramar hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto. Kwankwaso ya bayyana hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a matsayin babban abin takaici, yana mai kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin. A cewar rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto, mutane 77 ne ke cikin kwale-kwalen da ya kife yayin da yake ɗauke da manoma da sauran fasinjoji zuwa gonakins