AMMASCO RADIO NEWSROOM

politics

INEC ta bai wa Adeleke takardar nasara a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Osun

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya ( INEC ) ta bai wa Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke , da mataimakinsa, Kola Adewusi , takardun shaidar nasara bayan lashe zaɓen Gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta 2026 . An gabatar da takardun shaidar nasarar ne a hedikwatar INEC ta jihar da ke Osogbo , inda Kwamishinan Ƙasa na INEC mai kula da Jihar Osun, Farfesa Yinka Ajayi , ya jagoranci bikin. Gabatar da takardun ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Osun , yayin da Kola Adewusi ya zama zaɓaɓɓen mataimakin gwamna.

APM ta lashe kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 20 a Bauchi

Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta lashe dukkan kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 20 a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a faɗin Jihar Bauchi ranar Litinin. Shugabar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BSIEC), Jummai Abubakar, ce ta bayyana sakamakon zaɓen. Ta ce baya ga kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 20, jam’iyyar APM ta kuma lashe kujerun kansiloli 319 daga cikin 323 da aka fafata a jihar. Rahotanni sun ce wasu daga cikin jam’iyyun adawa sun kaurace wa zaɓen, lamarin da ya bai wa APM damar lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomin jihar.

Jam'iyar APM ta cinye zaben kujerun Kananan hukumomi 20 na Jihar Bauhci

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC) ta bayyana cewa APM ta kuma lashe kujerun kansiloli 319 daga cikin 323. Shugabar hukumar, Jummai Abubakar, ta ce dukkan ‘yan takarar APM 20 sun samu nasara bayan kammala kada kuri’a, kirga kuri’u da tattara sakamako. Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya soki jam’iyyun adawa kan kaurace wa zaben, yana mai cewa sun yi hakan ne saboda tsoron faduwa. Gwamnan ya bayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar cikin kwanciyar hankali, tare da jaddada muhimmancin kananan hukumomi wajen samar da ci gaba da kyakkyawan shugabanci.

. Ayyukan Tinubu sun nuna cancantar sake zaɓensa a 2027 – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci a sake zaɓensa a shekarar 2027, bisa la’akari da sauye-sauyen tattalin arziki da ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta aiwatar. Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman, Tunde Rahman , ne ya bayyana hakan yayin wani rangadin ayyukan gwamnati a Jihar Nasarawa. Ayyukan Raya Ƙasa Rahman ya ce ayyukan tituna, gadoji da cibiyoyin lafiya da tawagar ta gani a Nasarawa da Benue na daga cikin nasarorin da aka samu sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar. Ya ƙara da cewa sauye-sauyen g

Matar Gwamnan Jihar Osun ta jagoranci zanga-zangar Mata kan tashe -tashen hankula da kamen Yan jam'iyarsu gabanin zaben Gwamnan jihar

Uwargidan Gwamnan Jihar Osun, Titilola Adeleke, ta jagoranci zanga-zangar mata a jihar domin nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin kame-kame ba tare da ka’ida ba da kuma tashin hankula, gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar. Matan, wadanda suka fito daga kungiyoyin ’yan kasuwa da masu sana’o’i daban-daban, sun yi tattaki daga hanyar Osogbo zuwa Ilobu, inda suka nufi hedikwatar rundunar ’yansandan jihar da ke Osogbo. Adeleke ta bukaci ’yansanda su gudanar da bincike kan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da take zargi da hannu wajen tashin hankulan da ake samu a jihar. Ta

INEC ta tsawaita wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan takarar Gwamna da na Majalisun Jihohi da zasu fafata a zaben 2027

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta tsawaita wa’adin miƙa sunayen ’yan takarar kujerar gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi da za su fafata a babban zaɓen ƙasa na Fabrairu 2027. Wa’adin miƙa sunayen ’yan takarar, wanda bisa sabon jadawalin zaɓe aka tsara zai ƙare ranar Asabar, 8 ga Agusta 2026, yanzu an tsawaita shi zuwa ranar Talata, 11 ga Agusta 2026. Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon buƙatun da jam’iyyun siyasa suka gabatar na neman ƙarin lokaci domin kammala aikin miƙa sunayen ’yan takararsu. A wani ci gaba, INEC ta sanar da masu kaɗa ƙuri’a da suka nemi sauya k

SERAP ta bukaci ‘yan takarar shugaban ƙasa 19 su bayyana kadarorinsu kafin zaɓen 202

Ƙungiyar SERAP ta buƙaci dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa 19 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta sanar sunayensu, da su bayyana cikakkun bayanan kadarorinsu da basussukan da ake binsi, da na iyalansu sannan kuma, da na ‘ya’yansu da ba su kai shekara 18 ba, gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027. SERAP ta kuma buƙaci ‘yan takarar da su bayyana halastattun hanyoyin da suka samo manyan kadarorin da suke da su, tare da barranta mansu da sayen ƙuri’u da kuma bada cin hanci a Lokacin zaɓe. Ƙungiyar, a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktanta, Kolawole Oluwadare, ya fitar, ta ce ta yi wa

Wike: A Siyasa, Babu Mai Ƙarfafa Abokin Hamayya

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa babu ɗan siyasar da zai yi niyyar ƙarfafa abokin hamayyarsa a lokacin fafatawar siyasa, domin kowa yana ƙoƙarin kare muradunsa da bunƙasa tasirinsa. Wike ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da manema labarai a Abuja, yayin da yake martani kan kalaman Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa, "komai halal ne a siyasa" ( all is fair in politics ). Ministan ya ce a tsarin siyasa, abin da 'yan siyasa ke yi shi ne neman hanyoyin da za su ƙarfafa matsayinsu da kuma cimma manufofinsu, ba wai su taimaka wa abokan hamayyarsu su fi ƙarfi b

INEC Ta Fara Nuna Takardun Shaidar Karatu Da Bayanan 'Yan Takarar Shugaban Ƙasa Na Zaɓen 2027

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara nuna wa jama'a takardun shaidar karatu da bayanan sirri na 'yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu domin babban zaɓen shekarar 2027 . Takardun da aka wallafa sun haɗa da na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima , waɗanda jam'iyyar APC ta tsayar takara. Bisa bayanan da INEC ta wallafa, Shugaba Tinubu ya kammala digirin farko (B.Sc.) a fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration) daga Jami'ar Chicago da ke Amurka a shekarar 1979 . Takardun sun kuma nuna cewa ya yi hidimar bautar ƙasa (NYSC) a Jihar Oyo tsakanin

Obi da Kwankwaso na da kusan kashi 70 cikin 100 na damar samun nasara a zaɓen 2027 - Lawal

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal, ya ce tikitin takarar shugaban ƙasa na haɗin gwiwa tsakanin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 fiye da idan kowannensu ya tsaya takara daban. Lawal ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Symfoni TV, wadda aka fitar a ranar Asabar. A cewarsa, idan Obi da Kwankwaso suka haɗa kai a tikiti ɗaya, suna da kusan kashi 70 cikin 100 na damar samun nasara, yayin da ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu kusan kashi 50 cikin 100, sannan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ba zai s

Gwamnonin Kudu maso Gabashin Kasar nan biyar sun amince tare da mara wa Shugaba Tinubu baya a neman wa'adi na biyu

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas biyar sun cimma matsaya ta mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a wa'adi na biyu. Uzodimma, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas, ya bayyana hakan ne yayin wani taro da Majalisar Dattawan Jihar Imo da sarakunan gargajiya a Owerri. Ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna ƙwazo wajen aiwatar da ayyukan ci gaba a yankin ƙarƙashin manufar Renewed Hope, yana mai cewa al'ummar yankin na duba aikin gwamnati ne ba siyasa ba. A cewarsa, gwamnonin yankin sun yanke

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir, ya gargadi 'yan Najeriya da kada su zaɓi Atiku a 2027

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya buƙaci 'yan Najeriya da kada su goyi bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana zarginsa da gudanar da siyasa bisa kabilanci. Lawal ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar waya da ya yi da jaridar The PUNCH a daren Laraba yayin da yake mayar da martani kan takaddamar da ta kunno kai kan tikitin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Adamawa. Ya yi zargin cewa Atiku ne ke jagorantar yunƙurin maye gurbin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar, Suleiman Omar, da

Majalisar Wakilai Ta Ƙaddamar da Tsarin Ƙara Bai Wa Mata Damar Shiga Siyasa – Tajudeen Abbas

Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa Majalisar ta samar da wani tsari na musamman da ke da nufin ƙara bai wa mata damar shiga harkokin siyasa da kuma tsayawa takara a Najeriya. Abbas ya ce sabon tsarin zai bambanta da yadda ake gudanar da tsarin takara ga sauran ’yan siyasa, inda za a fara aiwatar da shi a matsayin gwaji na wasu shekaru kafin a tantance tasirinsa da yadda ya dace da tsarin siyasar ƙasar. Ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin Majalisar na inganta wakilcin mata a matakan shugabanci da kuma ƙarfafa shigarsu cikin harkokin siyas

Fantami Ya Bayyana Abin Da Zai Fi Ba Muhimmanci Idan Ya Zama Gwamnan Gombe

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa idan ya samu damar zama Gwamnan Jihar Gombe, zai mayar da hankali wajen amfani da ilimi da fasahar zamani domin magance matsalar rashin tsaro da kuma bunƙasa ci gaban jihar. Pantami ya ce gwamnatin da zai jagoranta za ta yi amfani da ƙwarewa da fasaha wajen inganta tsaro, jawo masu zuba jari, bunƙasa tattalin arziki da samar da damarmaki ga matasa. Ya kuma bayyana cewa gogewar da ya samu a matsayin shugaban Hukumar NITDA da kuma Ministan Sadarwa za ta taimaka masa wajen aiwatar da manufofin ci

Gbajabiamila ya nemi shugaban hukumar bogi Adeniyi Adeyemi ya biya shi diyyar Naira biliyan 15 kan zargin bata masa suna

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya buƙaci Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da ikirarin jagorantar wata hukumar bogi a Nijeriya, ya biya shi diyyar Naira biliyan 15 kan zargin ɓata masa suna. A cikin takardun ƙarar da aka shigar, Gbajabiamila ya ce kalamai da zarge-zargen da Adeyemi ya yi a kansa sun bata masa suna da mutunci, tare da jawo masa illa a idon jama’a. Saboda haka, ya buƙaci kotu ta umarci Adeyemi da ya biya shi diyyar Naira biliyan 15 saboda abin da ya bayyana a matsayin ɓata suna, tare da bayar da wasu umarni da suka dace domin kare martabarsa. Lamarin

Atiku ya bukaci a dakatar da Umahi tare da gudanar da bincike mai zaman kansa kan mutuwar Mary Habila

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya umarci Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya sauka daga muƙaminsa na wucin gadi har sai an kammala bincike kan mutuwar Mary Habila, wata matashiya mai shekara 26 da ta rasu a gidan ministan da ke Uburu, Jihar Ebonyi. Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da binciken lamarin. Ya ce akwai buƙatar a tabbatar da cewa binciken ya kasance mai zaman kansa, gaskiya da kuma adalci, yana mai zargin cewa gwamnati ba ta nu

Jajircewar uwargudan Shugaban kasa Remi Tinubu ne Allah ya saka Mata ta Zama Matar shugaban kasa

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce Allah ne ya saka wa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, saboda jajircewa da ƙwazonta lokacin da take mamba a majalisar dattawa. Barau ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar ranar Talata, bayan Sanata Abdul Ningi ya ba da shawarar a riƙa ɗaukar sunan sanatoci da su ka halarta a ƙarshen zaman domin karrama waɗanda ke zama har zuwa rufe zama. A cewarsa, Oluremi Tinubu ce kan kasance ta farko wajen zuwa majalisar, kuma tana zama har zuwa ƙarshen zaman, yana mai cewa wannan jajircewa ce Allah ya saka mata da matsayin uw

ADC da Atiku sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli

Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar , sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli , domin ƙalubalantar hukuncin da wata ƙaramar kotu ta yanke kan shari'ar da ke gabansu. Matakin na zuwa ne bayan rashin gamsuwa da hukuncin da aka yanke a baya, inda ɓangarorin biyu suka buƙaci Kotun Koli ta sake nazarin shari'ar tare da yanke hukuncin ƙarshe kan lamarin. Ana sa ran Kotun Koli za ta sanya ranar sauraron ƙarar bayan kammala dukkan matakan shigar da takardun da suka dace. Har zuwa yanzu, ba a fitar da cikakken bayani kan ranar da kotun za ta fara sau

Jamian yan sanda sun shirya gurfanar da Adeniyi adeyemi mutumin da ya kirkiri hukumar bogi da sunan fadar shugaban kasa

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Talata bisa zargin kafa wata hukumar bogi da ya danganta da Fadar Shugaban Ƙasa. Ana zargin Adeyemi da bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), wadda hukumomi suka ce ba ta da wata halastacciyar amincewa daga gwamnati. Shi da wasu mutum biyu na fuskantar tuhume-tuhume guda takwas da suka haɗa da ƙirƙirar takardun bogi, yin sojan gona da sauran laifuka masu alaƙa da yaudara. Binciken ‘yan sanda ya nuna c

Kara kudin jarabawar WAEC da NECO zai kara yawan yaran da ba sa zuwa makarant a Najeriya- Atiku

Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki rahotannin da ke cewa Gwamnatin tarayya ta amince da sanya kuɗin jarabawar WAEC da NECO zuwa N50,000 ga kowane ɗalibi daga shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce wannan mataki tare da ƙarin kuɗin makarantun Unity Colleges zai ƙara jefa iyaye cikin wahala tare da hana miliyoyin yara samun ilimi. Ya bayyana cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke da mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, yana mai cewa ƙara