INEC ta kara wa'adin mika sunayen 'yan takara a zaben 2027
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da tsawaita wa’adin gabatar da sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya domin babban zaɓen shekarar 2027 da karin kwanaki uku. A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Lahadi, ta ce sabon wa’adin zai ƙare da ƙarfe 12:00 na dare ranar Talata, 14 ga Yuli, 2026, maimakon ranar Asabar, 11 ga Yuli, 2026 da aka tsara tun farko. Sanarwar, wadda shugaban kwamitin wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a na INEC, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan ƙorafin da ƙungiyar Inter-Part
