AMMASCO RADIO NEWSROOM

security

Mazauna Zamfara Sun Ce Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama da 30

Mazauna ƙauyen Birnin Tudu da ke ƙaramar hukumar Gummi a Jihar Zamfara, sun ce sun kashe sama da ’yan bindiga 30 a wani artabu da ya ɗauki tsawon kwanaki uku, bayan da wasu mahara ɗauke da makamai suka kai wa al’ummar yankin hari.

Najeriya Ta Yanke wa Mutum 21 Hukuncin Ɗauri Kan Laifukan Ta’addanci

Najeriya ta ci gaba da gudanar da shari’o’in masu zargin aikata laifukan ta’addanci, inda a ranar 16 ga Oktoba aka yanke wa mutum 21 hukuncin ɗauri kan laifuka daban-daban da suka shafi ta’addanci, ciki har da wani ɗan ƙasar China, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.

Hukumomin tsaro sun ƙara tsaurara matakan tsaro a sansanonin NYSC, makarantu da guraren ibada bayan samun rahoton sirri

Hukumomin tsaro sun ƙara tsaurara sa ido a makarantu, sansanonin horas da matasa na NYSC, wuraren ibada da sauran wuraren da ake ganin suna cikin haɗari, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ’yan ta’adda na shirin kai hare-hare cikin haɗin gwiwa a sassa daban-daban na ƙasar. Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta bayar da wani gargaɗin tsaro da aka yaɗa zuwa sassa daban-daban na rundunar a faɗin ƙasar, inda ta yi gargadin yiwuwar hare-haren da aka shirya kaiwa da ka iya zo daidai da komawar ɗalibai makarantu a zangon karatu na shekarar 2026/2027. A cewar sanarwar ’yan sandan, bayanan sirrin da