AMMASCO RADIO NEWSROOM

security

Rundunar ‘yansandan ta kasa reshen Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike domin gano wasu malaman Addinin Musulunci shida da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara a Zamfara.

Rundunar ‘yansandan ta kasa reshen Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike domin gano wasu malaman Addinin Musulunci shida da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara a Zamfara. Rahotanni dai sun ce malaman suna hanyarsu ta komawa gida bayan zuwa wani taron addu’a na Jam’iyyar APC a Zamfara. ‘Yansandan sun ce tuni suka baza jami’ansu domin ceto malaman da aka sace. ’Yan bindiga sun sace limaman Musulunci shida a kan hanyar Dakko–Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura ta Jihar Zamfara. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar jiya Asabar, lokaci

Yan sanda sun kama Matar da ta yada cewa Opay zai daina aiki a ranar 31 ga watan Augusta

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta kama Hafsat Abubakar, mai shekara 27, bisa zargin ƙirƙira da yaɗa wata takardar bogi da ke cewa kamfanin OPay zai daina aiki. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Anietie Iniedu, ya bayyana cewa an kama Hafsat ne ranar 4 ga Satumba 2026, bayan OPay ta kai ƙorafi ga rundunar ‘yansanda a ranar 31 ga Agusta. Ya ce cibiyar yaƙi da laifukan yanar gizo ta ‘yansanda ta gudanar da binciken ƙwaƙƙwafi na Internet, inda aka gano cewa takardar ta samo asali ne daga wani shafin X da Hafsat Abubakar ke amfani da shi. ‘Yansandan sun ce takardar ta bogi ce kuma an gabatar da it

Yadda Rundunar yan sanda jihar Kano tayi nasarar cafke mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Danshagamu

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani mutum mai suna Ibrahim Khalil Danshagamu , mazaunin unguwar Gaida da ke Karamar Hukumar Kumbotso a jihar Kano. Rundunar ta ce da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, 8 ga Satumba, 2026 , ta samu rahoton gaggawa daga kwamandan kungiyar sa-kai ta Gaida cewa wasu ’yan daba da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidan marigayin da ƙarfi tare da kai masa hari da wasu abubuwa masu kaifi. Bayan samun rahoton, jami’an sashen ’yan sanda na Kumbotso sun garzaya wurin da lamarin ya faru. An garzaya da wanda ak

Rundunar sojin kasar nan ta ce jami’anta sun ceto mutane 36 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka ’yanta’adda da dama a sassa daban-daban

Hedikwatar tsaron kasarnan ta ce dakarunta sun ceto mutane 36 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka ’yanta’adda da dama a sabbin ayyukan soji da suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar. Daraktan Ayyukan Yaɗa Labaran Sojoji, Manjo Janar Michael Onoja ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, kan ayyukan sojin da aka gudanar tsakanin 31 ga Agusta zuwa 3 ga Satumban, 2026. Ya ce dakarun sun hallaka wani ɗanta’adda a ranar 1 ga Satumba, bayan da suka tarwatsa wani abin fashewa da aka dasa a kan babbar hanyar samar da kayayyaki ta Miyanti-Banki Junction a Bama, Jihar

Rundunar Yan sandan Kano ta tura sabbin jami'a 250 da ta horar zuwa Kananun hukumomin dake iyakar jihar don inganta tsaro

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta rarraba jami’an ’yan sanda 250 da suka kammala horo na tsawon wata guda zuwa ƙananan hukumomin da ke kan iyaka, a mataki na ƙarfafa tsaron yankunan. Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Bakori ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin bikin yaye rukuni na biyu na jami’ai 250 da suka kammala horon yaƙi da kuma sarrafa makamai. Yan sandan da aka horar sun hadar da masu mukaman kwanstabil (Constables )da Kofur na ’Yan Sanda (Police Corporal). Ya bayyana cewa an gudanar da horon a lokaci guda a sansanonin 9 PMF da ke Hotoro, da kuma 52 PMF da ke Challawa inda ya

EFCC ta kori sama ma’aikatanta 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata bisa zargin aikata rashawa da almundahanar kuɗi

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa, EFCC, ta bayyana cewa ta kori sama da ma’aikatan ta 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata bisa zargin aikata rashawa da almundahanar kuɗi. Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ganawa da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yan jarida. Olukoyede ya ce, tuni aka gurfanar da biyar daga wadanda ake zargin tare da shirin gurfanar da karin wasu jami'an. Ya ce hukumar ta kuma ƙaddamar da sabbin matakai na ƙarfafa ɗa’a da gaskiya tsakanin ma’aikatanta, ciki har da tsarin kula da kyaututtuka da kuma wajibcin bayyana kada

NAPTIP ta ce ta ceto yara sama da 180 da aka yi safararsu daga jihohin Kaduna, Anambra, Benue, Nasarawa da wasu wurare a ƙasar nan

Hukumar ta bayyana cewa wasu ƙungiyoyin masu fataucin yara na yaudarar iyaye ta hanyar bayyana kansu a matsayin ma'aikatan ƙungiyoyin fararen hula masu tallafa wa yara da ilimi, sannan su tafi da yaran da sunan ba su ilimi da tallafi. A baya-bayan nan, an ceto wasu yara uku da aka kwaso daga Kajuru a jihar Kaduna a wani gini da ke Onitsha ta jihar Anambra, yayin da aka kuma gano wani yaro a hannun wata ma'aikaciyar lafiya. NAPTIP ta ce wasu daga cikin yaran da aka ceto an kai su gidajen marayu inda aka rika sayar da su ga mutane da sunan ɗaukar yara reno. Hukumar ta ce tana ci gaba da farautar

An kama wata mata Mrs. Iyabo Sowunmi, da zargin kokarin shigar da haramtattun miyagun kwayoyi gidan gyaran hali dake jihar Ogun

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya reshen Jihar Ogun ta kama wata mata, Mrs. Iyabo Sowunmi, bisa zargin ƙoƙarin shigar da wasu ƙwayoyi da ake zargin haramtattu ne zuwa Cibiyar Tsare Fursunoni da ke Ibara, Abeokuta, domin ɗanta, Dare Sowunmi, wanda ake tsare bayan yanke wa hukuncin kisa. Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya, reshen Jihar Ogun, Olayinka Odukoya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Odukoya ya ce an kama Sowunmi da misalin ƙarfe 1:33 na rana ranar Juma'a, 28 ga Agusta, 2026, yayin da ake gudanar da bincike

Operation FANSAN YAMMA sun kashe wani babban mataimakin shugaban 'yan ta'adda tare da kwato bindigogi a jihar Katsina

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, karkashin Operation FANSAN YAMMA, sun yi nasarar ajalin wani babban mataimakin shugaban 'yan ta'adda tare da kwato bindigogi, alburusai da babura yayin wani samame a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina. An gudanar da samamen ne jiya asabar yayin da dakarun Sector 2 suka kutsa cikin wasu maboyar 'yan ta'adda da aka gano a yankin. A wata sanarwa da jami'in yada labarai na rundunar hadin gwiwar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar yau Lahadi, ya ce dakarun sun fuskanci turjiya mai tsanani daga 'yan ta'adda dauke da makamai yayin samamen. Sai

’Yan Sandan Jigawa sun ƙwato shanu, babura da wasu kayayyaki a samame da suka gudanar a sassan jihar

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama mutane 17 kan zargin aikata laifuka daban-daban, tare da ƙwato shanu, babura da wasu kayayyaki a samame da ta gudanar a sassan jihar. Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar. Sanarwar ta bayyana cewa, an kama mutanen ne a samame daban-daban da aka gudanar a ƙananan hukumomin Malam Madori, Gwaram, Garki, Kiyawa, Taura, Birniwa, Dutse, Ringim, Miga, Kazaure da Roni, bisa zargin sata, fasa shaguna, satar shanu, lalata kadarori da fashi da makami. Rundunar ta ce, daga cikin kayayyakin da aka ƙwa

Yadda Yan bindiga suka save Sarkin Noman Kano Alhaji Yusuf Nadabo tare da kashe mutane uku a Chiromawa

’Yan bindiga sun kashe mutane uku, sun raunata biyar tare da sace Sarkin Noman Jihar Kano, Alhaji Yusuf Nadabo Chiromawa, a wani hari da suka kai garin Chiromawa da ke Karamar Hukumar Garun Malam. Shugaban Karamar Hukumar Garun Malam, Alhaji Aminu Salisu Kadawa, ya tabbatar da faruwar lamarin. Kadawa ya ce, ya samu rahoton shigowar ’yan bindigar garin da misalin ƙarfe 11:00 na daren Asabar, inda suka nufi gidan Sarkin Noman tare da yin harbe-harbe kan mai uwa dawabi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku da raunata wasu biyar. Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa, waɗanda suka jik

Sojojin sun hallaka yan ta'adda 6 tare da kwato shanun da aka sace a Lakwaya da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo a nan Kano.

ojojin sun hallaka yan ta'adda 6 tare da kwato shanun da aka sace a Lakwaya da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo a nan Kano. Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran ƙaramar hukumar Gwarzo, Auwalu Musa Yola, ya fitar yau Laraba. Ya ce, lamarin ya faru ne yayin wani sumame da jami’an tsaron suka gudanar a yankin Lakwaya, inda suka tunkari ’yan bindigar. Sanarwar ta ce, Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwarzo, Hon. Mani Tsoho, ya ziyarci yankin na Lakwaya domin yaba wa jami’an tsaro kan matakin. Shugaban ya buƙaci al’ummar yankin da su ci gaba da taka tsantsan tare da isar da sahihan bayanai ga jami’an

Sojoji sun dakile yunƙurin garkuwa da mutane a Zamfara, sun kuɓutar da fararen hula

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da ke aiki a Arewa maso Yammacin ƙasar sun dakile wasu yunƙurin garkuwa da mutane da ’yan ta’adda suka yi a sassa daban-daban na Jihar Zamfara, tare da kuɓutar da fararen hula daga hannun maharan. Rundunar ta ce a ranar 17 ga Agustan 2026 , dakarunta sun kai ɗauki bayan samun rahoton sace mutane a kan hanyar Gurusu zuwa Anka . Sojojin sun bi sahun maharan cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta musu watsar da mutanen da suka yi garkuwa da su tare da tserewa zuwa cikin daji. A yayin aikin, an samu nasarar kuɓutar da mutane bakwai , waɗanda suka haɗa da mata

Sojoji sun kuɓutar da wata mata da ’ya’yanta biyu da ’yan ta’adda suka sace a 2017

Dakarun Sojin Najeriya sun kuɓutar da wata mata tare da ’ya’yanta biyu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka yi garkuwa da su a shekarar 2017 a Jihar Borno. Rahotanni sun ce an kuɓutar da su ne a yayin wani samame na bincike da dakarun suka gudanar a kusa da Gadar Amuda da ke jihar. Wata kafar yaɗa labaran yaƙi da ta’addanci mai suna Zagazola Makama ta ruwaito cewa dakarun sun tare mutanen ne da misalin ƙarfe 6:30 na safe ranar 14 ga Agustan 2026 , yayin da suke gudanar da sintiri a yankin. An ce jami’an sun gano matar da ’ya’yanta biyu yayin sintirin, inda suka kuɓutar da su tare da kai su wurin

Yan bindiga sunyi garkuwa tare da harbin wasu mutane a garin Lakwaya dake karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano

Al'ummar garin Lakwaya da ke Karamar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano sun kwana cikin zullumi bayan harin da 'yan bindiga suka kai garin a daren Juma'a. Bayanai daga mazauna garin da dama sun zargi cewa 'yan bindigar sun shiga Lakwaya, inda suka harbi mutane tare da yin garkuwa da wasu da kuma korar shanu. Huzaifa Ibrahim Lakwaya ya bayyana cewa, 'yan bindigar sun harbi mutane biyu, sun yi garkuwa da mutane biyu tare da korar shanu, yayin da Couch Figo Lakwaya ya tabbatar da harbin mutane biyun, yana mai cewa daya an harbe shi a hannu, daya kuma a fuska, sannan ya ce an tafi da wasu mutane da bai s

Rundunar sojin Najeriya ta bude kofar daukar sabbin ma'aikata a bangaren Short service

Rundunar Sojin Najeriya ta buɗe damar neman aikin soja na Short Service na Shekarar 2027 ga fararen hula da jami’an soji masu aiki da suka cika sharudda. Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar ɗaukar ma’aikata da ta fitar a ranar Talata, inda ta gayyaci ’yan Najeriya da suka cancanta da su nemi gurbin zama jami’an soja ta tsarin Short Service Combatant Commission. A cewar sanarwar, waɗanda suka yi nasara za su yi aiki ne a ɓangaren Combat Arms, wanda ya haɗa da rundunonin Infantry da Armour, da kuma ɓangaren Combat Support Arms, wanda ya ƙunshi Artillery, Engineers, Signals da Inte

Yan sanda a Jihar kwara sun kama wata mata da ake zargin da kashe yar kishiyarta

Rundunar ’yan sandan Jihar Kwara ta kama wata mata mai suna Sadiat Yunusa, bisa zargin ta shake ’yar mijinta mai shekaru uku, Ummaiyat har ta mutu a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar. A cewar ’yan sandan, wadda ake zargin ta bayyana cewa mijinta ya yi watsi da ita da ’ya’yanta uku, tare da fifta kishiyarta da yar ta ta. ’Yan sandan sun ce wadda ake zargin ta yaudari yarinyar ne har ta ja ta zuwa cikin gonaki da ke kusa, inda ake zargin ta kashe ta bayan wata doguwar takaddamar. Da take ƙarin bayani kan lamarin, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta c

PSC Ta Miƙa Sabbin ’Yan Sanda 50,000 Ga Rundunar ’Yan Sanda.

Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda (Police Service Commission – PSC) ta miƙa sabbin jami’an ’yan sanda 50,000 da aka ɗauka aiki ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya domin fara horo, a wani mataki na ƙara ƙarfafa ƙarfin aikin tsaro a faɗin ƙasar. A cikin wata sanarwa da Hukumar ta fitar, ta ce ɗaukar sabbin jami’an ya gudana ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu , tare da bin dukkan tanade-tanaden doka da suka shafi aikin. Hukumar ta bayyana cewa an miƙa jerin sunayen waɗanda suka yi nasara a aikin ɗaukar ma’aikatan ga Rundunar ’Yan Sandan Najeriya domin a tura su zuwa cibiyoyin horo da

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Borno ta kama mutane biyar kan zargin yanka matattun shanu da sayar da namansu ga mutane a birnin Maiduguri

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Borno ta kama mutane biyar kan zargin yanka matattun shanu da sayar da namansu ga ɗaiɗaikun mutane da mahauta masu tsire a birnin Maiduguri. Wannan na cikin sanarwar da Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar jiya litinin. Sanarwar ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a tsohuwar kasuwar shanu ta Maiduguri, bayan samun sahihan bayanan sirri, inda ake zarginsu da yanka shanun da suka mutu tare da sayar da namansu ga jama'a. Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin kama su, an same su da gawar matacciyar saniya da ake zargin suna shirin

Ƴan bindiga sun kai hari kotu a Katsina, alƙali ya tsere ta taga

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari a wata kotun shari'a da ke ƙauyen Gwarjo , a Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina, inda Alƙali Mohammed Muktar ya tsira bayan ya tsere ta taga kafin maharan su kutsa cikin kotun. Rahotanni sun ce mazauna yankin sun ga maharan suna tunkarar kotun a ranar 29 ga Yuli , lamarin da ya sa alƙalin ya fice cikin gaggawa ta taga kafin su isa. Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun shiga kotun suna harbe-harbe tare da tambayar inda alƙalin yake. A cewarsa, wani direban babur mai ɗaukar fasinja ( acaba ) ne ya taimaka wa Alƙali Muktar ya tsere daga yanki