Wani babban jami'in kungiyar ISWAP mai kula da harkokin kudi ya mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai a Jihar Borno
Wani babban jami'in kungiyar ISWAP mai kula da harkokin kudi ya mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai a Jihar Borno, sakamakon ci gaba da hare-haren da sojoji ke kai wa maboyar 'yan ta'addan a Arewa maso Gabas. A cikin wata sanarwa, rundunar sojin Najeriya ta ce mutumin ya mika wuya da misalin karfe 6:45 na safiyar Juma'a a kan hanyar Ladari–Jegarawa–Tunokalia da ke kan babbar hanyar Gamboru–Wulgo. Binciken farko ya nuna cewa mutumin shi ne babban jami'in kula da kudaden sansanin ISWAP da ke Jubillaram, inda yake da alhakin tafiyar da kudade da kuma samar da kayayyakin kungiyar. Sojojin sun
