Sojojin Najeriya Sun Kashe ’Yan Ta’adda Biyu, Sun Kwace Makamai a Zamfara
Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun Operation FANSAN YAMMA sun kashe ’yan ta’adda biyu tare da kwato bindigogi, alburusai da babura yayin wani samame a yankin Garin Kaso, ƙaramar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara . A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, dakarun sun yi artabu mai tsanani da ’yan ta’addan a ranar Juma’a, 14 ga Agusta 2026, inda suka kwato bindigogi biyu, magazina biyu, harsasai tara da babura biyu . Rundunar ta ce daga bisani wasu ’yan ta’adda sun yi ƙoƙarin yi wa sojojin kwanton bauna daga maɓoyarsu, amma dakarun sun yi nasarar fatattakar su tare da jikkata wasu daga cik
