Gwamnatin Kano Ta Miƙa Takardun Mallakar Filaye Ga Masu Bai Wa Gwamna Shawara da Masu Ɗauko Rahoto
Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa takardun mallakar filaye (Certificate of Occupancy – C of O) ga masu bai wa gwamna shawara da kuma masu ɗauko rahoto daga ma'aikatu, a wani biki da aka gudanar a Coronation Hall da ke Gidan Gwamnatin Kano. Bikin ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da kuma waɗanda suka amfana da shirin. Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan Ƙasa da Tsare-tsare na Jihar Kano, Abduljabbar Muhammad Umar , ya ce gwamnatin jihar ta aiwatar da shirin ne domin cika alƙawarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka ga mukarraban gwamnatinsa. Ya bayyana cewa an gudanar da aikin tantance
