Najeriya Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Ɗan Ƙasarta A Afirka Ta Kudu, Ta Nemi Bincike Cikin Gaggawa
Gwamnatin Najeriya, ta hannun Ofishin Jakadancinta da ke Johannesburg , ta yi Allah wadai da kisan wani ɗan ƙasar, Ibeh Chika Simon , wanda ya rasa ransa yayin wani samamen da 'yan sandan Afirka ta Kudu suka kai a yankin Bellville da ke Cape Town a ranar 23 ga Yuli . A cikin wata sanarwa, jakadancin ya ce mutuwar marigayin ta faru ne a yanayi da ke haifar da tambayoyi masu yawa. Haka kuma, wani ɗan Najeriya, Egwabor Patrick Chuks , ya samu munanan raunuka bayan harbin bindiga da aka yi masa a lokacin samamen. Jakadancin ya bayyana matuƙar damuwarsa kan lamarin, yana mai zargin jami'an tsaron d
