Ku janye Kudurin Dokar kafafen Sada zumunta ko ku fuskanci Shari'a - Gargadin SERAP ga Majalisar kasa
SERAP ta bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta janye kudirin gyaran Dokar Kare Bayanai ta Najeriya na 2026, tana mai cewa wata hanya ce ta bayan fage da gwamnati ke son amfani da ita wajen sanya ido da takaita 'yancin bayyana ra'ayi a kafafen sada zumunta. SERAP ta yi gargadin cewa za ta shigar da kara a kotu idan aka zartar da kudirin dokar a yadda yake yanzu ko kuma da wani salo mai kama da shi. Kudirin dokar, wanda Sanata Ned Nwoko (APC, Delta North) ya dauki nauyin gabatarwa, na neman tilasta wa kafafen sada zumunta, masu sarrafa bayanai (data controllers) da masu aiwatar da sarrafa bayana
