Wike: Yawancin Ayyukan Da Muka Kammala A Abuja Tsofaffin Ayyuka Ne Da Aka Yi Watsi Da Su
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa mafi yawan ayyukan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kammala a Abuja tsoffin ayyuka ne da aka yi watsi da su tun gwamnatocin da suka gabata. Da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Wike ya ce gwamnatin ta ba da fifiko wajen kammala ayyukan da ta gada kafin fara sabbin ayyuka. Ya bayyana cewa wasu daga cikin ayyukan sun shafe shekaru tsakanin 15 zuwa 16 ba a kammala su ba, amma gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba da umarnin a farfaɗo da su domin kada a bar muhimman ayyukan gwamnati su lalace. A cewarsa, kusan kashi 60
