IMF zai bai wa Nijar bashin dala miliyan 203 domin farfaɗo da tattalin arziƙinta
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya sanar da cimma matsaya da mahukuntan Nijar kan bayar da sabon rancen kuɗi har dala miliyan 203, domin taimaka wa ƙasar wajen farfaɗo da tattalin arziƙinta da aiwatar da gyare-gyare a wannan fanni cikin shekaru uku masu zuwa. Sanarwar IMF, wadda shugabar tawagar asusun da ta ziyarci Nijar, Julia Bersch, ta sanya wa hannu, ta ce an cimma yarjejeniyar ne yayin tattaunawar da wakilan asusun suka yi da mahukuntan ƙasar a birnin Yamai, babban birnin Nijar. A cewar sanarwar, yarjejeniyar ta shafi tsawon watanni 38, amma ana jiran amincewar hukumar gudanarwar IMF
