AMMASCO RADIO NEWSROOM

world

Harin Bam Ya Kashe Mutum Shida a Damascus na Ƙasar Syria

Aƙalla mutum shida sun mutu, yayin da wasu 22 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a wani gidan shan shayi da ke cike da jama'a a tsakiyar birnin Damascus , babban birnin ƙasar Syria. Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Syria sun ruwaito cewa, bam ɗin ya tashi ne a wani gidan shan shayi da ke gundumar Hejaz , mai nisan kusan mita 100 daga ginin Ma'aikatar Shari'a ta ƙasar. Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Syria ta bayyana cewa an dasa abin fashewar ne a cikin gidan shayin kafin ya tashi, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da jikkata mutane da dama. Har zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki

Iran Ta Yi Allah-Wadai da Barazanar Isra'ila Kan Khamenei

Iran ta yi Allah-wadai da kalaman da Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz , ya yi kan Mojtaba Khamenei , inda ta bayyana su a matsayin barazana da ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amir Saeed Iravani , ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa da ya aikewa Sakatare Janar da kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya. A cikin wasiƙar, Iravani ya ce barazanar da aka yi wa Mojtaba Khamenei shaida ce ta abin da ya kira ta'addancin da gwamnati ke aiwatarwa, yana mai zargin cewa yin shiru da Kwamitin Tsaro ya yi na ƙara ƙarfafa Isra'ila. Tun da farko,

Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Iran Kazem Gharibabadi ya ce Tehran zata yi amfani da kadarorinta da amurka zata saka wajen biyan manyan bukatunta

Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Iran Kazem Gharibabadi ya ce Tehran za ta yi amfani da wasu kadarorinta da aka daskarar a Qatar wajen siyan kayayyakin bukatun ƙasar, bayan tattaunawar aka kammala a Doha, da ya yi bitar yarjejeniyar fahimtar juna da ta dakatar da yakin da ke tsakanin Iran da Amurka. Ɗaya daga cikin batutuwa da ke ƙkarkashin yarjejeniyar fahimtar juna da ta dakatar da yakin da ke tsakanin Iran da Amurka, Washington ta amince a saki wasu ƙadarori da kuɗaɗen Iran da aka daskarar a matsayin wani ɓangare na aiwatar da yarjejeniyar. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem

Sojojin Burkina Faso a ranar Laraba sun ce sun daƙile hare-haren da ƙungiyoyin ‘yanta’adda tare da kashe fiye da mahara 400

Sojojin Burkina Faso a ranar Laraba sun ce sun daƙile hare-haren da ƙungiyoyin ‘yanta’adda suka kai wasu sansanonin soji a ranar 30 ga Yuni, inda aka kashe fiye da mahara 400. Sojojin sun daƙile harin ne bayan samun taimako daga jiragen sama. A cikin wata sanarwa da Hedkwatar Sojin Burkina Faso ta fitar ranar Laraba da daddare, ta ce ‘yanta’addan sun kai hare-hare kan sansanonin soji da kuma jami’an sa-kai don kare ƙasa a ƙauyukan Gayeri da ke yankin Sirba, da Solhan da Sebba a yankin Liptako. A cewar rundunar, sojojin ƙasa, tare da goyon bayan jiragen sama, sun mayar da martani nan-take ga ha

Magoya Bayan Norway Sun Yi Murnar Kaiwa Zagayen 'Yan 16 na Kofin Duniya

Dubban magoya bayan tawagar Norway sun fito kan titunan birnin Oslo domin murnar nasarar da ƙasarsu ta samu ta kai wa zagayen 'yan 16 na Gasar Cin Kofin Duniya. Rahotanni sun ce dimbin jama'ar da suka halarci bikin ya haifar da cunkoso da kuma lalacewar wasu kayayyakin more rayuwa a wasu sassan birnin. Norway ta samu gurbin ne bayan nasarar da ta yi a wasanta na baya, lamarin da ya jawo farin ciki da murnar magoya baya a faɗin ƙasar. Hukumomin birnin sun ce suna tantance irin barnar da aka samu, tare da kira ga jama'a da su gudanar da bukukuwa cikin lumana da kiyaye dukiyoyin jama'a.

Chelsea Ta Kammala Ɗaukar Marco Palestra Daga Atalanta

Chelsea ta tabbatar da ɗaukar Marco Palestra daga Atalanta BC kan yarjejeniyar da rahotanni suka ce ta kai kusan fam miliyan 47, ciki har da wasu ƙarin sharuɗɗa. Ɗan wasan mai shekara 21 ya sanya hannu kan kwantiragin shekara shida, tare da zaɓin ƙarin shekara guda. Shi ne kuma ɗaya daga cikin sababbin 'yan wasan da ƙungiyar ta ɗauka tun bayan naɗin Xabi Alonso a matsayin sabon koci. Rahotanni sun ce Chelsea ta yi nasarar doke Inter Milan wajen ɗaukar Palestra, bayan ta gabatar da tayin da ya fi na ƙungiyar ta Italiya. Ana kuma sa ran Chelsea za ta ci gaba da neman ƙarin 'yan baya domin ƙarfaf

Afirka ta Kudu: An Kama Kimanin Mutum 900 Bayan Zanga-zanga

Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu sun bayyana cewa an kama kusan mutum 900 bayan zanga-zangar da aka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar. A cewar hukumomi, an kama mafi yawan mutanen ne bisa zargin laifukan da suka haɗa da karya dokokin shige da fice da wasu laifuka, yayin da aka ce yawancin zanga-zangar ta gudana cikin lumana. Sai dai wasu daga cikin gangamin sun rikide zuwa tashin hankali, lamarin da ya sa aka ƙara matakan tsaro a wasu yankuna. Shugaban ƙasar, Cyril Ramaphosa , ya ce gwamnati na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki, tare da kira ga jama'a da su kiyaye doka da oda.

Iran Ta Ce Za Ta Mayar da Martani ga Duk Wata Barazana

Ministan Harkokin Wajen Iran , Abbas Araghchi , ya bayyana cewa ƙasarsa za ta mayar da martani cikin gaggawa idan aka fuskanci wata barazana ga al'ummarta ko shugabanninta. Kalaman nasa sun biyo bayan wasu bayanai daga gwamnatin Isra'ila kan yiwuwar ɗaukar matakin soja idan aka samu sabon hari. Araghchi ya kuma yi kira da a mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin ɓangarorin, yana mai cewa duk wani kaucewa abin da aka amince da shi na iya ƙara dagula rikicin. Har yanzu dai ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar tsakanin Iran da Isra'ila, yayin da ƙasashen duniya ke kira ga ɓangarorin da su guji mata

Iran Ta Sanar da Rufe Tehran Domin Gudanar da Jana'izar Ayatollah Ali Khamenei

Gwamnatin Iran ta sanar da cewa za a rufe birnin Tehran na ɗan lokaci domin sauƙaƙa gudanar da jana'izar marigayi Ayatollah Ali Khamenei , tare da bai wa masu makoki damar halartar tarukan jana'izar cikin sauƙi. Hukumomin ƙasar sun kuma ayyana ranar zaman makoki ta ƙasa, yayin da aka tsara gudanar da bukukuwan jana'izar a biranen Tehran , Qom da Mashhad kafin a binne marigayin a Mashhad. Rahotanni sun nuna cewa za a kuma gudanar da tarukan tunawa da marigayin a wasu biranen ƙasar Iraq , yayin da ake sa ran dubban mutane za su halarci jana'izar. ( Al Jazeera )

Kotun Ƙolin Amurka Ta Yi Watsi da Ƙalubalantar Haƙƙin Zama Ɗan Ƙasa Ta Haihuwa

Kotun Ƙolin Amurka ta yanke hukuncin da ya tabbatar da ci gaba da aiwatar da haƙƙin zama ɗan ƙasar Amurka ta hanyar haihuwa, bayan ta yi watsi da wani ƙoƙarin sauya tsarin. Alƙalan kotun mafi rinjaye sun bayyana cewa wannan haƙƙi yana da tushe a kundin tsarin mulkin ƙasar, yayin da wasu alƙalan suka nuna rashin amincewa da hukuncin. Shugaban ƙasar, Donald Trump , ya bayyana rashin gamsuwarsa da hukuncin, amma ya ce Majalisar Dokoki na da ikon duba batun ta hanyar kafa doka. A gefe guda kuma, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun yi maraba da hukuncin kotun, suna mai cewa ya tabbatar da kariyar

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Kira da a Ƙara Kai Agaji ga Venezuela Bayan Girgizar Ƙasa

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa mutane da dama a Venezuela na buƙatar agajin gaggawa, musamman abinci da matsuguni, bayan girgizar ƙasa da ta afku a ƙasar. A cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar, lamarin ya haifar da tsaiko ga ayyukan yau da kullum a wasu yankuna, yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan ceto da kai agaji. Rahotanni sun kuma nuna cewa an sake buɗe wata tashar jirgin ruwa domin sauƙaƙe isar da kayan agaji ga mutanen da abin ya shafa. Hukumomi sun ce adadin waɗanda suka rasu ya ƙaru, yayin da ake ci gaba da neman wasu da ba a gano ba, tare da ci gaba da

Rahotanni: Robert Lewandowski Na Dab Da Komawa Chicago Fire

Robert Lewandowski na dab da kammala komawa Chicago Fire FC bayan karewar kwantiraginsa da FC Barcelona. Rahotanni sun ce ana sa ran ɗan wasan mai shekara 37 zai sanya hannu kan kwantiragin shekara biyu da ƙungiyar ta gasar Major League Soccer (MLS), duk da cewa wasu ƙungiyoyi ma sun nuna sha'awar ɗaukarsa. Idan yarjejeniyar ta kammala, Lewandowski zai ƙara wa Chicago Fire ƙarfi yayin da ƙungiyar ke shirin ci gaba da fafatawa a kakar wasa ta bana.

Iran ta kai hari kan sansanin Ali al-Salem da ke Kuwait, da kuma hedikwatar rundunar ruwa ta Amurka da ke Bahrain

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito cewa wani jami’in Amurka ya tabbatar da cewa Iran ta harba makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuƙa zuwa wasu ƙasashe makwabta, ciki har da Bahrain da Kuwait. Tuni rundunar IRGC ta Iran ta sanar cewa ta kai hari kan wuraren sojojin Amurka, inda ta ce ta nufi sansanin Ali al-Salem da ke Kuwait, da kuma hedikwatar rundunar ruwa ta Amurka da ke Bahrain. Rundunar ta ce ta kai waɗannan hare-hare ne da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

An rantsar da Andy Burnham a Majalisar Dokokin Birtaniya

An rantsar da Andy Burnham a matsayin sabon ɗan Majalisar Dokokin Birtaniya mai wakiltar mazaɓar Makerfield bayan nasararsa a zaɓe. Ya samu kyakkyawar tarba da tafi daga 'yan jam'iyyar Labour yayin da ya shiga zauren majalisar domin yin rantsuwar kama aiki. Burnham ya yi rantsuwar ne tare da wasu sabbin 'yan majalisa biyu, Lara Bird ta jam'iyyar SNP da Douglas Lumsden na jam'iyyar Conservative. Yayin da yake shiga zauren majalisar, ya nuna godiya ga 'yan majalisar da suka tarbe shi ta hanyar murmushi da sunkuyar da kai.

Gwamnatin Nijar Ta Zargi Faransa da Ɗaukar Nauyin Harin Filin Jirgin Sama na Niamey

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar nauyin harin da aka kai a filin jirgin saman Yamai da safiyar Alhamis. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar ta fitar kuma aka karanta a gidan talabijin na RTN a birnin Niamey, gwamnatin ta yi zargin cewa “masu ɗauke da makamai da Macron ke biya” ne suka kai wani mummunan hari da ya kashe aƙalla sojoji 11 da fararen hula biyu. Duk da haka, gwamnatin ƙasar ba ta bayar da wata shaidar da za ta tabbatar da wannan zargin ba, kuma Faransa ba ta ce uffan kan batun ba har yanzu. A cewar sanarwar, maharan waɗanda ake zargi suna sanye

Za a Gurfanar da Kyaftin ɗin Morocco Achraf Hakimi Kan Zargin Fyade

Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Morocco, Achraf Hakimi, zai gurfana a gaban kotu a Faransa bayan masu gabatar da ƙara sun amince da ci gaba da shari’ar da ake yi masa kan zargin fyade. Wata mata mai shekara 24 ta zargi ɗan wasan bayan na Paris Saint-Germain da yi mata fyade a gidansa da ke birnin Paris a shekarar 2023. Ofishin mai gabatar da ƙara a Nanterre, da ke yammacin Paris, ya fara gudanar da bincike kan lamarin tun a watan Maris na shekarar 2023. A watan Fabrairun 2026, wani alƙali mai bincike ya bayar da umarnin a ci gaba da shari’ar, yayin da rahotanni daga kafofin yaɗa labarai na

Netanyahu Ya Ce Isra’ila Za Ta Ci Gaba da Zama a Kudancin Lebanon

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba ta da niyyar janye sojojin Isra’ila daga kudancin Lebanon da kuma yankunan da take kallon su a matsayin shingen kariyar tsaro. Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin da wasu mambobin majalisarsa ke ci gaba da sukar yarjejeniyar da ake ƙoƙarin cimmawa tsakanin Amurka da Iran. Ya ce kamar yadda Isra’ila ta samu nasarar dawo da tsaro da zaman lafiya a yankunan da ke kan iyaka da Zirin Gaza, haka kuma tana da burin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a birane da ƙauyukan arewacin ƙasar. “Kiyaye tsaron al’ummomin da ke a

Taliban Ta Haramta Wa Ma’aikatan Gwamnati Zuwa Aiki da Manyan Wayoyi

Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta haramta wa ma’aikatan gwamnati da na hukumomin tsaro zuwa wuraren aiki da manyan wayoyi, a wani sabon mataki da ta ce an ɗauka domin ƙara mayar da hankali kan ayyukan gwamnati. Ma’aikatan gwamnati da dama sun shaida wa BBC cewa an umarce su da kada su kawo wayoyin hannu na zamani zuwa ofisoshi da wuraren aiki, yayin da wasu suka ce an gargade su da su rage amfani da wayoyin har ma a gidajensu. Wani jami’in gwamnatin Taliban ya bayyana cewa manufar matakin ita ce tabbatar da cewa ma’aikata suna mayar da hankali kan ayyukan da aka ɗora musu maimakon ɓata lokaci

An Ji Fashe-Fashe da Harbe-Harbe a Filin Jirgin Sama na Niamey

Niamey, Nijar – Rahotanni daga babban birnin Jamhuriyar Nijar sun bayyana cewa an ji ƙarar fashe-fashe da harbe-harbe a filin jirgin saman Niamey, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin da matafiya. Bayanan farko sun nuna cewa jami’an tsaro sun gaggauta mayar da martani tare da tura ƙarin jami’ai zuwa filin jirgin saman domin shawo kan lamarin da kuma tabbatar da tsaro a yankin. Sai dai zuwa wannan lokacin, hukumomi ba su fitar da cikakken bayani a hukumance kan musabbabin lamarin ba. Haka kuma, ba a tabbatar da ko akwai waɗanda suka rasa rayukansu ko suka jikkata sakamakon abin

Trump Ya Gargaɗi Isra’ila Kan Ci Gaba da Kai Hare-Hare a Lebanon

Shugaban Amurka, Donald Trump , ya yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da hare-haren da take kai wa Lebanon, yana mai cewa lokaci ya yi da za a nuna haƙuri domin kauce wa ƙara rura wutar rikici a yankin. Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Truth Social, sa’a guda bayan harin da Isra’ila ta kai yankin Dahiyeh da ke Beirut. Ya ce bai kamata harin ya faru ba, musamman a daidai lokacin da ake kusantar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran. Ya jaddada cewa wajibi ne bangarorin da ke rikicin su nuna takatsantsan, yana mai cewa kamar yadda bai kamata Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon