Aƙalla mutane uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka samu raunuka, sannan aka ƙona gidaje da babura a wani rikici tsakanin makiyaya da manoma a Paikon-Kore, da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada cewa ba za ta dawo da tsarin tallafin man fetur ba, duk da matsin tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta sakamakon tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.
Jami’an diflomasiyya daga Faransa, Belgium da Poland sun fuskanci hari daga wasu ’yan kama wuri zauna na Isra’ila yayin da suke ziyartar ƙauyen Taybeh da ke Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
An zaɓi Najeriya a matsayin mamba a Majalisar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHRC) na wa’adin shekarun 2027 zuwa 2029, bayan ta samu ƙuri’u 172 cikin ƙuri’u 181 da aka kaɗa a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.
Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira da a ƙara zuba jari wajen tallafa wa matan da ke zaune a karkara, domin bunƙasa noma, inganta samar da abinci da kuma ƙarfafa tattalin arziki.
Mahukuntan Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Koyon Shari’a ta Aminu Kano (AKCILS) sun musanta jita-jitar da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta cewa makarantar na hana ɗalibai mata masu sanya niƙabi shiga harabar kwalejin.
Akalla mutane biyu sun mutu, yayin da wasu 21 suka jikkata sakamakon hare-haren sama da Rasha ta kai kan birnin Kyiv, babban birnin Ukraine, inda aka samu katsewar wutar lantarki a sassa daban-daban na birnin.
Shugabannin ƙasashen duniya sun ci gaba da aika saƙonnin fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga Paparoma Leo, bayan an yi masa tiyatar da aka ce an cire wani ɓangare na huhunsa na dama a birnin Rome.
Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, yayin da hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen mutane ke ci gaba da zama babban ƙalubalen tsaro a sassan ƙasar.
Tsofaffin sojojin Najeriya sun toshe ƙofar shiga ofishin Hukumar Kula da Fanshon Sojoji da ke Abuja a ranar Talata, domin neman a sauya tsarin lissafa kuɗaɗen fanshonsu da kuma biyan buƙatunsu.
Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da ɗaukar yara ko amfani da su a ayyukan yaƙi, matakin da ka iya janyo takaita wasu nau'o'in tallafin soji da haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da fara rarraba ruwan sha daga ma’ajiyar Goron Dutse Reservoir zuwa sassan birnin Kano, bayan shafe sama da shekaru 30 ba ta aiki. Gwamnan ya bayyana farfaɗo da ma’ajiyar a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen inganta samar da ruwan sha ga al’ummar Kano. Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Dahiru Muhammad Hashim, ya ce ma’ajiyar na da damar adana kusan lita miliyan 39.8 na ruwa. Ya ce ana tura ruwan daga matatar Challawa zuwa Goron Dutse, daga inda ake rarraba shi ga al’ummomin sassa daban-daban na birnin Kano. A cewarsa, kamfan
Kamfanin Dillancin Labaran Japan, Kyodo, ya ruwaito cewa wani babban jami’in gwamnatin Iran da ba a bayyana sunansa ba ya ce ƙasar na shirin buɗe Mashigar Hormuz cikin mako guda, domin sassauta takunkumin da aka kakaba mata. A cewar rahoton, matakin na daga cikin yunƙurin Tehran na komawa kan teburin tattaunawa da Amurka domin kawo ƙarshen yaƙin. Kyodo ya ce jami’in ya bayyana cewa Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran da Jagoran Addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei, sun amince da wannan shawara. Rahoton ya ƙara da cewa masu shiga tsakani sun riga sun gabatar da shawarar Iran ga gwamnatin Amurka. Jami’in y
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa, ta ɗage yajin aikin gargaɗin da ta shirya yi zuwa ƙarshen watan Oktoba, domin bai wa Gwamnatin Jihar Jigawa ƙarin lokaci ta warware matsalolin da suka shafi jami’ar. A baya ƙungiyar ta sanya ranar Talata, 15 ga Satumba, 2026, wato yau, domin fara yajin aikin gargaɗi kan batutuwan da ba a warware su ba, musamman aiwatar da yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta shekarar 2025, da kuma biyan basussukan albashin da ake bin mambobinta. Wannan sabon ci gaba ya biyo bayan sabunta tattaunawa tsakanin ƙungiyar da
Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli ta Jihar Legas (LAWMA) ta sanar da cewa, daga mako mai zuwa, za a kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu yana sayen kaya daga ‘yan kasuwar da ke gudanar da kasuwanci ba bisa ka’ida ba a kan tituna, tsakiyar tituna, gefen tituna, hanyoyin masu tafiya a kafa da sauran wuraren jama’a da ba a amince da yin kasuwanci a cikinsu ba. Hukumar ta ce matakin ya yi daidai da tanadin sashe na 151, karamin sashe na 2 na Dokar Kare Muhalli da Gudanar da Muhalli ta Jihar Legas ta shekarar 2017. Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na LAWMA, Dr. Muyiwa Gbadegesin,
Mahukunta a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo sun tabbatar da mutuwar yara ƴan makaranta aƙalla 24 sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a wasu makarantu biyu a birnin Bukavu da ke gabashin ƙasar. Lamarin ya janyo ruɗani sosai, yayin da aka samu rahoton mutuwar wasu manya tare da jikkatar mutane da dama da aka garzaya da su asibitoci domin samun kulawa. Rahotanni sun ce gobarar ta kuma lalata gidaje kusan 300, yayin da har yanzu hukumomi ba su gano musabbabin tashin wutar ba. Hotunan da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna ƙananan yara kwance a asibiti, wasu na fama da raunukan ƙunar wu
Sakataren Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), Olufemi Oke-Osanyintolu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:56 na dare a ranar Alhamis, a agini mai lamba 42, Governors Road, Aboru, dake ƙaramar hukumar Alimosho ta jihar. Oke-Osanyintolu ya ce nan take aka tura ƙungiyar Alpha Eagle Response Team ta hukumar zuwa wurin bayan samun kiran neman agaji. A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa ginin ya ruguje ne a lokacin da ake rushe shi da hannu. Ya ƙara da cewa: “Bayan isowar jami’an agajin farko, sun tabbatar
Jami’ar Kimiyya da Fasaha Ta Aliko Dangote dake Wudil, ta karyata rahoton da ke cewa an samu jinkiri wajen tura wasu daga cikin ɗalibanta zuwa shirin yi wa ƙasa hidima na NYSC.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Abdullahi Datti Abdullahi, ya fitar ranar 9 ga Satumba 2026, jami’ar ta ce babu ɗalibin da ya kammala karatu a watan Satumba 2025, domin a lokacin ne kawai suka kammala jarabawar shekarar ƙarshe. Ta ce sai an kammala tantance sakamako da sauran matakan amincewa kafin a tabbatar da kammala karatu.
Jami'ar Ta bayyana cewa ta tura ɗalibai 1
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Alhaji Aminu Atiku a matsayin sabon Sarkin Zamfaran Zurmi, kuma Sarkin Masarautar Zurmi. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce gwamnan ya amince da naɗin ne bayan shawarar masu zaɓen sarki na Masarautar Zurmi, bisa tanadin al’adu da dokokin jihar. Alhaji Aminu Atiku, wanda ke riƙe da sarautar Dangaladiman Zurmi, shi ne zai zama Sarkin Zamfaran Zurmi na 21. Ya maye gurbin marigayi Alhaji Bello Suleiman, wanda ya rasu a ranar 31 ga watan Agustan 2026. Sabon sark