NUJ reshen Kano ta yi tir da harin da aka kai wa ’yan jarida da ke aikin dauko rahoton taron jam’iyyar APC a kano a ranar asaba
Kungiyar ’Yan Jaridu ta Kasa (NUJ), reshen Jihar Kano, ta yi tir da harin da aka kai wa ’yan jarida da ke aikin dauko rahoton taron jam’iyyar APC a Filin Wasa na Sani Abacha da ke Kano a ranar Asabar. Kungiyar ta bayyana harin, wanda ake zargin wasu ’yan daba ne suka kai wa ’yan jarida tare da lalata motar gidan rediyon kasa, Pyramid FM Kano, a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, tare da cewa barazana ce ga ’yancin aikin jarida. A cikin wata sanarwa da Shugaban NUJ na Jihar Kano, Comrade Suleiman Abdullahi Dederi, da Sakatarenta, Comrade Hauwa Suleiman Zahradeen, suka sanya wa hannu, ku
