‘Yan kasuwar man fetur sun yi watsi da rahoton cewa matatar Dangote na shirin dakatar da sayar da fetur ga ‘yan kasuwar da ke shigo da man daga waje
‘Yan kasuwar man fetur da masu shigo da shi sun yi watsi da rahoton cewa matatar Dangote na shirin dakatar da sayar da fetur ga ‘yan kasuwar da ke shigo da man daga ƙasashen waje. Sun zargi matatar da ƙoƙarin hana shigo da fetur, tare da kalubalantar ta da ta gabatar da hujjar cewa fetur ɗin da ake shigowa da shi Najeriya bai cika ƙa’idojin inganci ba. Rahotanni sun ce matatar na nazarin takaita sayar da fetur ga manyan ‘yan kasuwa da ke ci gaba da shigo da man daga waje. Matatar na zargin wasu ‘yan kasuwa da haɗa fetur ɗin da suka saya daga Dangote da na waje, lamarin da take ganin zai iya h
