NHRC Ta Yi Gargadi Kan Kalaman Tsokana Gaban Zaɓen Osun da na 2027
Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa ( NHRC ) ta nuna damuwa kan yawaitar kalaman ƙiyayya, kalaman tsokana, barazanar tashin hankali da kuma tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a gabanin zaɓen gwamna da za a gudanar a Jihar Osun, da kuma babban zaɓen shekarar 2027. A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Sakataren Hukumar, Tony Ojukwu , ya jaddada buƙatar hukumomin da abin ya shafa su ɗauki matakin gaggawa domin dakile kalaman da ka iya ƙara tayar da hankali tare da kawo cikas ga gudanar da zaɓe cikin lumana. NHRC ta musamman ja hankalin jama’a kan wasu kalamai masu rarrabuwar kai da ake dangantawa
