Kwankwaso Ya Soki Kalaman Sheikh Jingir Kan Batun Muslim-Muslim
Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso , ya ce wasu kalaman malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir , na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Najeriya. A wata sanarwa da Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana damuwarsa kan kalaman Sheikh Jingir da ya yi a wani taro a Kano a ƙarshen mako. Kwankwaso ya jaddada cewa al’ummar Kano ba sa goyon bayan kalaman da za su iya raba kan ’yan Najeriya , yana mai cewa bai kamata a yi amfani da murya ko matsayi wajen furta kalaman da za su raunana haɗin kan ƙasa ba. A kwanakin baya ne kafafen sada zumunta da na yaɗa la
