APM/PDP Ta Fara Rajistar Masu Sa Kai Domin Yaƙin Neman Zaɓen 2027
Ƙungiyar Makinde Reset Nigeria Volunteers and Reset Agents ta sanar da fara rajistar masu sa kai a faɗin ƙasar domin tallafa wa burin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde , na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin haɗakar jam'iyyun APM/PDP . A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a Abuja, ta ce an buɗe rajistar ne tun daga ranar Litinin, kuma ta samu karɓuwa daga masu sha'awa a jihohi 36 na Najeriya, Babban Birnin Tarayya (FCT) da kuma 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje. Ƙungiyar ta bayyana cewa shirin na da nufin gina wata babbar cibiyar masu sa kai a faɗin ƙasar domin
