Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama mutane 1,860 tare da ƙwace kilogiram 5,409.814 na miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano tsakanin Janairu da Satumba 2026.
Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) sun bayyana cewa ƙasar ta samu sabbin manyan makamai bayan yaƙin da ta yi da Amurka da Isra’ila, tare da gargaɗin cewa za ta mayar da martani mai tsanani idan aka sake kai mata hari.
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya shawarci Najeriya da kada ta dawo da tsarin tallafin man fetur, inda ya buƙaci gwamnati ta mayar da hankali wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi domin rage tasirin hauhawar farashin makamashi.
Akalla mutane biyu sun mutu, yayin da wasu 21 suka jikkata sakamakon hare-haren sama da Rasha ta kai kan birnin Kyiv, babban birnin Ukraine, inda aka samu katsewar wutar lantarki a sassa daban-daban na birnin.
Shugabannin ƙasashen duniya sun ci gaba da aika saƙonnin fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga Paparoma Leo, bayan an yi masa tiyatar da aka ce an cire wani ɓangare na huhunsa na dama a birnin Rome.
Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, yayin da hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen mutane ke ci gaba da zama babban ƙalubalen tsaro a sassan ƙasar.
Tsofaffin sojojin Najeriya sun toshe ƙofar shiga ofishin Hukumar Kula da Fanshon Sojoji da ke Abuja a ranar Talata, domin neman a sauya tsarin lissafa kuɗaɗen fanshonsu da kuma biyan buƙatunsu.
Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da ɗaukar yara ko amfani da su a ayyukan yaƙi, matakin da ka iya janyo takaita wasu nau'o'in tallafin soji da haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce tana aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da kuɓutar da wani magidanci, matarsa da jaririyarsu da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a unguwar Millennium City da ke Kaduna.
Lauyoyin Isa Ali Pantami sun bai wa INEC wa’adin kwanaki uku ta sanya sunansa cikin jerin ’yan takarar gwamnan Gombe na PDP a zaɓen 2027, ko kuma su garzaya kotu
An yi Allah-wadai a sassa daban-daban na duniya kan matakin Amurka na ƙara kakaba takunkumin kuɗi ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC. Kotun ta ICC da kuma Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya sun bayyana matakin hana mu’amalar kuɗi da kotun a matsayin wani hari kan tsarin tabbatar da adalci a matakin ƙasa da ƙasa. Kasashen Canada da Japan da wasu ƙasashen Turai sun sake jaddada goyon bayansu ga kotun, wadda ke da alhakin bincike da gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata manyan laifuka, ciki har da laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama. A nasa ɓangaren, Sakataren
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sanar da cewa za ta ƙaddamar da gangamin yaƙin neman sake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Kaduna ranar 24 ga Oktoban 2026. A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, ya fitar, APC ta ce taron na Kaduna zai zama farkon zagayen gangamin neman goyon baya a faɗin jihohi 36 na Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja. Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta ɗauki wasu matakai masu wahala na gyaran tattalin arziki, waɗanda a cewar jam’iyyar, gwamnatocin
An ji wata babbar ƙarar fashewa a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Riyadh, babban birnin Saudiyya, a daidai lokacin da ake samun rahotannin ƙaruwa da hare-haren makamai masu linzami da ake dangantawa da ƙungiyar Houthi ta Yemen. Ya zuwa yanzu, hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da cewa an kai hari a filin jirgin saman ba. Sai dai rahotannin farko sun nuna cewa an fara kwashe mutane daga filin jirgin. Kamfanonin jiragen sama na Etihad Airways da Qatar Airways sun soke wasu jirage da dama da za su tashi zuwa Riyadh, ciki har da wasu da aka tsara gudanarwa har zuwa ranar Litinin. Wannan na zuwa
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya sanar da cimma matsaya da mahukuntan Nijar kan bayar da sabon rancen kuɗi har dala miliyan 203, domin taimaka wa ƙasar wajen farfaɗo da tattalin arziƙinta da aiwatar da gyare-gyare a wannan fanni cikin shekaru uku masu zuwa. Sanarwar IMF, wadda shugabar tawagar asusun da ta ziyarci Nijar, Julia Bersch, ta sanya wa hannu, ta ce an cimma yarjejeniyar ne yayin tattaunawar da wakilan asusun suka yi da mahukuntan ƙasar a birnin Yamai, babban birnin Nijar. A cewar sanarwar, yarjejeniyar ta shafi tsawon watanni 38, amma ana jiran amincewar hukumar gudanarwar IMF
Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen fidda gwani da ya samar da Bashir Abdullahi Gaddafi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ADC mai neman kujerar Akko a Majalisar Wakilan Tarayya a zaɓen 2027. Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Vera E. Ibrahim, ta umarci a gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a mazabar cikin kwanaki 21. Haka kuma, kotun ta bayar da umarnin janye takardar shaidar nasarar zaɓen da aka bai wa Gaddafi nan take. Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Adamu Hassan Kashere ya shigar, inda ya ƙalubalanci yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani da ya samar da Gaddafi a
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya (ACF) ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta rage mayar da hankali kan shirye-shiryen zaɓen 2027, tare da karkata hankalinta wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar. Ƙungiyar ta bayyana cewa ci gaba da kai hare-hare, kashe-kashe, garkuwa da mutane da lalata hanyoyin samun abin dogaro da kai da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke yi, na barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin Najeriya. A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran ƙungiyar, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya fitar, ACF ta nuna damuwarta kan abin da ta bayyana a matsayin rash
Dakarun Sojin Najeriya da ke aikin yaƙi da ’yan bindiga a ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma sun sanar da lalata wasu bama-bamai guda uku da aka dasa a Jihar Zamfara. Kakakin rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’a. Ya ce haɗin gwiwar jami’an tsaro ya yi nasarar gano tare da kwance bama-baman da aka dasa a babbar hanyar Magami zuwa Dansadau da ke jihar. A cewarsa, an gudanar da aikin ne tare da taimakon sashen kwance bama-bamai na rundunar ’yan sandan Najeriya, kuma an kammala aikin ba tare da an samu as
A watan Disambar 2024 ne Manchester City ƙarƙashin jagorancin Pep Guardiola ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Liverpool a filin Anfield, inda magoya bayan Liverpool suka riƙa yi wa kocin waƙar cewa: “Za a kore ka da safe.” A wancan lokacin, da wuya a yi tunanin cewa za a kori Guardiola, duk da cewa Manchester City na shirin yin rashin nasara a wasanta na huɗu a jere a gasar Premier League, lamarin da ba kasafai yake faruwa ba a ƙarƙashin jagorancinsa. A martaninsa ga magoya bayan Liverpool, Guardiola ya ɗaga yatsunsa shida, domin tunasar da su kofunan Premier League shida da ya lashe tare da Man
Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce ta fara ƙoƙarin gano na’urorin da ke ɗauke da bayanan muryoyin matuƙan jirgi da kuma bayanan jirgin da ya yi hatsari a yankin Igbokoda, da ke Ƙaramar Hukumar Ilaje a Jihar Ondo. Babban jami’in kula da ƙa’idoji da tantancewa na rundunar, Air Vice Marshal Ebimobo Ebiowe, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wurin da hatsarin ya faru a ranar Juma’a. Jirgin mai saukar ungulu, wanda ke gudanar da aikin yau da kullum daga Benin, babban birnin Jihar Edo, zuwa Legas, ya faɗo cikin wata fadama kusa da sansanin Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya da ke Igbokoda a ranar