ADC ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa
Jam’iyyar hamayya ta ADC a Najeriya ta ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, a wani mataki na shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027. Yayin ƙaddamar da kwamitin a Abuja, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya bayyana waɗanda aka naɗa a matsayin masu kishin ƙasa da kuma gogaggun mutane a harkokin siyasa da tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya. Sanata Augustine Okwudiri Akobundu ne zai jagoranci kwamitin, tare da taimakon wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. El-Rufai dai na fuskantar bincike
