AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Birtaniya Ta Yi Kira ga Hamas Ta Ajiye Makamai

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, ya yi kira ga ƙungiyar Hamas da ta mika makamanta tare da rusa abin da ya kira “ginshiƙan ayyukan ta’addanci” na ƙungiyar. Miliband ya ce, a ƙarƙashin shirin zaman lafiya mai ɗauke da yarjejeniyoyi 20, Hamas ba za ta taka wata rawa a shugabancin Gaza a nan gaba ba. Ya bayyana cewa Isra’ila na da haƙƙin rayuwa cikin tsaro ba tare da fargaba ba, amma ya ce sama da mutum 70,000 aka kashe a Gaza, ciki har da yara kusan 20,000. Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya ya kuma ce ana ci gaba da samun cikas wajen kai agajin jinƙai da kayan ceton rayuka zuwa

Kenya Ta Bai Wa Baƙin Haure Kwanaki 90 Su Daidaita Takardunsu

Gwamnatin Kenya ta bai wa baƙin haure da ke gudanar da ƙananan sana’o’i a ƙasar wa’adin kwanaki 90 su mallaki takardun zama, izinin aiki da kuma lasisin gudanar da kasuwanci. Kakakin Fadar Shugaban Ƙasar, Hussein Mohammed, ya ce za a gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar ofisoshin jakadancin ƙasashen da abin ya shafa, domin bai wa baƙin hauren damar daidaita takardunsu da harkokin kasuwancinsu cikin tsari. Ya ce gwamnati za ta yi amfani da kwanaki 90 masu zuwa wajen gudanar da aikin, kuma bayan cikar wa’adin za a fara tsaurara aiwatar da dokokin shige da fice. Matakin ya biyo bayan umarnin

Gwamnan Katsina ya gabatar da kasafin kuɗin N828.64bn na 2027 ga majalisar dokokin jihar

Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda ya gabatarwa majalisar dokokin jihar da daftarin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2027 , wanda ya kai Naira biliyan 828.64 a ranar talata domin amincewa. Kusan kashi 77 cikin 100 na kasafin kuɗin an ware shi ne domin ayyukan raya ƙasa. Kasafin kuɗin mi taken “Building Your Future IV” , ya ware Naira biliyan 637.91 , wato kashi 76.98 cikin 100 , domin ayyukan manyan ayyuka, yayin da aka ware Naira biliyan 190.73 , kwatankwacin kashi 23.02 cikin 100 , domin gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati. Adadin kasafin kudin ya ragu da Naira biliyan 69.23 idan aka

NAHCON Tana Tunatar da Maniyyatan Hajjin 2027 Kan Wa’adin Rajista

Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta sake tunatar da maniyyatan Hajjin 2027 cewa ranar 26 ga Satumba ce wa’adin ƙarshe na kammala rajista da biyan kuɗin aikin Hajjin. NAHCON ta yi wannan tunatarwa ne cikin saƙonnin da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, inda ta buƙaci maniyyatan da ba su kammala rajista ko biyan kuɗaɗen aikin Hajjin ba da su yi hakan kafin cikar wa’adin. Hukumar ta ce wa’adin ya yi daidai da jadawalin da hukumomin Saudiyya suka gindaya domin shirye-shiryen aikin Hajjin 2027. Ta ce kammala rajista da biyan kuɗaɗe cikin lokaci na da muhimmanci wajen daidaita bayanan mani

NEC Ta Sanya Ranar Zaɓukan Cike Gurbi

IHukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sanya ranar 19 ga watan Satumba domin gudanar da zaɓukan cike gurbi guda biyar a jihohin Gombe, Kano, Bauchi da Delta. Sakataren Yaɗa Labarai na Shugaban INEC, Tunde Oketola, ne ya tabbatar da hakan, inda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, cewa zaɓukan sun ƙunshi kujera guda ɗaya ta Majalisar Wakilai ta Tarayya da kuma kujerun majalisun jihohi guda huɗu. A cewarsa, za a gudanar da zaɓen kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a mazabar Gombe/Kwami/Funakaye ta Jihar Gombe. Yayin da zaɓukan kujerun majalisun jihohi za su gudana a m

Bene Mai Hawa Uku Ya Ruguje a Abuja

Wani bene mai hawa uku ya ruguje a yankin Wuse Zone 4 da ke Abuja, sa’o’i kaɗan bayan hukumomin kula da ci gaban birane sun rufe ginin tare da umartar mutanen da ke cikinsa su fice. Hotuna da bidiyoyin da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ginin ya ruguje, yayin da jama’a suka taru a wurin bayan faruwar lamarin. Kawo yanzu ba a bayyana musabbabin rugujewar ginin ba. Haka kuma, babu cikakken bayani kan ko akwai mutane a cikin ginin lokacin da ya ruguje, ko kuma ko akwai waɗanda tarkacen ginin ya danne. Sai dai Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta ce ta samu kiran gaggawa g

An Yi Jana’izar Mijin Shugabar Tanzania

An yi jana’izar Hafidh Ameir Hassan, mijin Shugabar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, a Kizimkazi da ke Zanzibar. Marigayin, wanda aka haifa a ranar 1 ga Janairu, 1946, ya rasu ne a ranar Litinin, 7 ga Satumba, bayan fama da matsalar zuciya. Mataimakin Shugaban Tanzania, Deogratius Ndejembi, ne ya sanar da rasuwar, inda ya ce Hafidh Ameir Hassan ya rasu da misalin ƙarfe 8:00 na safe agogon ƙasar. Ya rasu ne a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar, inda yake karɓar magani. Jana’izar marigayin ta gudana a garinsu na Kizimkazi, inda iyalai, ’yan uwa da sauran al’umma suka halarta domin yi ma

Birtaniya Ta Ce Isra’ila Na Aikata Kisan Kiyashi a Yammacin Kogin Jordan

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, ya ce gwamnatin ƙasar ta amince da cewa Isra’ila na aikata abin da ta kira kisan kiyashi a wasu sassan Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye. Da yake jawabi a Majalisar Dokokin Birtaniya, Miliband ya zargi gwamnatin Isra’ila da yin biris da abubuwan da ke faruwa a yankunan Falasɗinawa. Ya ce Birtaniya ta daɗe tana kallon matsugunan Isra’ila da ke Yammacin Kogin Jordan a matsayin waɗanda suka saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. Miliband ya kuma sanar da cewa gwamnatin Birtaniya ta ɗauki matsayar cewa mamayar da Isra’ila ke yi wa Yammacin Kogin Jordan ba t

Birtaniya Za Ta Hana Shigo da Kayayyakin Matsugunan Yahudawa

Gwamnatin Birtaniya na shirin hana shigo da kayayyakin da aka samar a matsugunan Yahudawa da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ciki har da kayayyakin amfanin gona. Matakin na cikin wasu sauye-sauyen da gwamnatin Birtaniya ke shirin yi kan manufofinta game da Isra’ila, yayin da take ƙara matsa lamba kan ƙasar dangane da faɗaɗa matsugunan Yahudawa a yankunan Falasɗinawa da aka mamaye. A makon da ya gabata, Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, ya shaida wa ’yan majalisar dokokin ƙasar cewa gwamnati na duba yiwuwar sauya wasu daga cikin tsare-tsaren da ke tsakaninta da Isra’ila. Gwamnato

An Kama Mutane 16 Kan Rikicin Ƙaramar Hukumar Dass.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama mutum kusan 16 da ake zargi da hannu a wani rikici da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu a Ƙaramar Hukumar Dass. Rundunar ta ce ana binciken waɗanda aka kama kan zargin haɗa baki wajen aikata laifi, tayar da tarzoma da kuma kisan kai. Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya shaida wa BBC cewa binciken farko ya nuna cewa lamarin ya fara ne a ranar 4 ga Satumban 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma. Ya ce wani mutum mai suna Ibrahim El-Safwan, wanda aka fi sani da Jabala’i, ya haɗa baki da wasu mutane tare da kai wa wani mai tuka babur mai kafa uku, Ab

Iyalin El-Rufai Sun Bai Wa Ministan Tsaro Wa’adin Kwanaki Bakwai

Iyalin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun bai wa Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, wa’adin kwanaki bakwai da ya janye wasu zarge-zargen da ya yi wa tsohon gwamnan ko kuma su ɗauki matakin shari’a a kansa. A wata sanarwa da ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai, ya fitar a madadin iyalan a ranar Litinin, ya ce Janar Musa ya yi zarge-zargen ne yayin wata hira kai tsaye da shirin Politics Today na Channels Television a ranar 3 ga Satumba. Sanarwar ta ce ministan ya zargi El-Rufai da shirya kashe mutane a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamnan jihar. Sai da

Merz Ya Ce Jamus Na Fuskantar Sauyi a Siyasar Jam’iyyu

Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce ƙasar na fuskantar wani gagarumin sauyi a tsarin siyasar jam’iyyu, bayan da jam’iyyar AfD ta masu tsattsauran ra’ayi ta samu gagarumar nasara a zaɓen jihar Saxony-Anhalt da ke gabashin ƙasar. Merz ya ce sakamakon zaɓen ya zama babban abin damuwa ga jam’iyyar CDU mai ra’ayin mazan jiya, yana mai cewa akwai buƙatar jam’iyyar ta gudanar da nazari mai zurfi kan dalilan da suka haifar da wannan sakamako. Da yake magana kamar yadda jaridar Bild ta ruwaito, Merz ya ce akwai buƙatar jam’iyyar ta ƙara kusantar jama’a tare da ƙara ƙoƙari wajen fahimtar mat

Mutane Biyar Sun Rasu A Hatsarin Jirgin Amazon Air A Miami

Aƙalla mutum biyar sun mutu, yayin da wasu biyar suka samu munanan raunuka bayan wani jirgin dakon kaya na kamfanin Amazon Air ya kauce daga titin saukar jirage yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jirgin sama na Miami International Airport da ke Amurka. Jirgin, samfurin Boeing 767-300 , ya yi hatsarin ne jim kaɗan kafin ƙarfe biyu na rana agogon ƙasar, wato ƙarfe 19:00 agogon GMT, bayan da ya tashi daga filin jirgin sama na Luis Muñoz Marín da ke San Juan, Puerto Rico. Rahotanni sun ce jirgin ya kuma bugi wasu motoci da ke kusa da wurin da hatsarin ya afku. Kamfanin Amazon ya bayyana cewa yana

Iran Ta Yi Barazanar Mayar Da Martani Kan Sabon Ƙudurin IAEA

Iran ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakan mayar da martani idan kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, IAEA, ya amince da sabon daftarin ƙudurin da ƙasashen Turai suka gabatar kan shirin nukiliyarta. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce ƙudurin na iya sake kai batun shirin nukiliyar Iran gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya. Baghaei ya zargi ƙasashen Turai da komawa ga batun shirin nukiliyar Iran a duk lokacin da suka kasa cimma wasu daga cikin manufofinsu, yana mai cewa hakan wata hanya ce ta ƙara matsin lamba kan Tehran. Y

Mijin Shugabar Tanzania Ya Rasu

Mijin shugabar ƙasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan, Hafidh Ameir Hassan, ya rasu a yau Litinin, 7 ga watan Satumban 2026. Mataimakin shugaban ƙasar Tanzania, Deogratius Ndejembi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau. Sanarwar ta ce Hafidh Ameir Hassan ya rasu ne yayin da yake karɓar magani a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar, sakamakon wata matsalar lafiya da ta shafi zuciya. An ce ya rasu ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe. Sanarwar ta ƙara da cewa tuni aka fara shirye-shiryen jana’izarsa, wadda za a gudanar a yankin Kizimkazi da ke Zanzibar.

Iran Ta Gargadi Koriya Ta Kudu Kan Shiga Ayyukan Soji A Mashigar Hormuz

Iran ta gargadi Koriya ta Kudu kan duk wani shiri na tura dakarunta ko shiga ayyukan soji a Tekun Fasha da mashigar Hormuz, tana mai cewa hakan zai haifar da mummunan sakamako . Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei , ne ya yi gargadin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da harshen Koriya. Baghaei ya ce Iran za ta ɗauki duk wani kasancewar sojojin Koriya ta Kudu ko shiga ayyukan soji a yankin a matsayin goyon bayan Amurka , tare da yin gargadin cewa hakan zai haifar da mummunan sakamako. Gargadin na Iran na zuwa ne yayin da gwamnatin Koriya ta Kudu ke nazarin

An Kai Sabon Hari Kan kamfanin man Saudiyya hari

Jaridar Financial Times ta ruwaito cewa an sake kai hari kan wasu cibiyoyin kamfanin mai na Saudiyya, Saudi Aramco, da ke birnin Jizan a ranar Litinin. Rahoton ya ce harin ya faru ne kusan wata guda bayan wani hari da ya taɓa ayyukan matatar man kamfanin da ke Jizan, yayin da ake ci gaba da tantance girman ɓarnar da sabon harin ya haddasa. Jizan, da ke kusa da iyakar Saudiyya da Yemen, na daga cikin wuraren da hare-hare suka fi kai wa a cikin rikicin yankin. Matatar man Jizan na da ƙarfin tace kusan ganga 400,000 na ɗanyen mai a kowace rana. Babban jami'in Aramco, Amin Nasser, ya ce hare-haren

An Nada Aminu Atiku Sabon Sarkin Zurmi

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Alhaji Aminu Atiku a matsayin sabon Sarkin Zamfaran Zurmi, kuma Sarkin Masarautar Zurmi. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce gwamnan ya amince da naɗin ne bayan shawarar masu zaɓen sarki na Masarautar Zurmi, bisa tanadin al’adu da dokokin jihar. Alhaji Aminu Atiku, wanda ke riƙe da sarautar Dangaladiman Zurmi, shi ne zai zama Sarkin Zamfaran Zurmi na 21. Ya maye gurbin marigayi Alhaji Bello Suleiman, wanda ya rasu a ranar 31 ga watan Agustan 2026. Sabon sark

Direbobi da ke bin titin Onitsha zuwa Owerri a Jihar Anambra sun koka kan yadda jami’an Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ke muzanta musu

Masu ababen hawa da ke bin titin Onitsha zuwa Owerri a Jihar Anambra sun koka kan yadda jami’an Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Anambra ke ci gaba da muzanta musu tare da kakaba musu tarar da suka ce ba ta dace ba, musamman a wuraren da titin ya lalace kusa da tashar People’s Club. Wasu daga cikin direbobin da suka zanta da jaridar Punch sun zargi jami’an hukumar da amfani da lalacewar titin wajen karbar kudade daga hannun masu ababen hawa. Sun ce ana karbar kudade tsakanin dubu N150 zuwa dubu N300 daga masu motoci na kashin kansu da direbobin tasi da na motocin haya da ke b

NUT reshen Karamar Hukumar Rogo a nan Kano ta ƙaddamar da shirin koyar da malamai 400 aikin sanyawa da gyaran na’urorin lantarki na Solar

Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa NUT reshen Karamar Hukumar Rogo a nan Kano ta ƙaddamar da shirin koyar da malamai 400 aikin sanyawa, kulawa da gyaran na’urorin lantarki na Solar. Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na Karamar Hukumar Rogo, Abdu Bako Abdullahi, ya fitar. Sanarwar ta bayyana cewa, Shugaban NUT na Karamar Hukumar Rogo, Malam Aliyu Suleiman, ya ce shirin zai bai wa malaman ƙarin ƙwarewar sana’a da za ta taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai. Malam Aliyu Suleiman ya ce malamai 400 za su amfana da shirin, inda za a koya musu yadda ake sanya na’urorin Solar, kul