AMMASCO RADIO NEWSROOM

Duniya

Mazauna Zamfara Sun Ce Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama da 30

Mazauna ƙauyen Birnin Tudu da ke ƙaramar hukumar Gummi a Jihar Zamfara, sun ce sun kashe sama da ’yan bindiga 30 a wani artabu da ya ɗauki tsawon kwanaki uku, bayan da wasu mahara ɗauke da makamai suka kai wa al’ummar yankin hari.

Tinubu da APC Za Su Ƙaddamar da Yaƙin Neman Zaɓen 2027 a Kaduna

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da shugabannin jam’iyyar APC, za su ƙaddamar da yaƙin neman sake zaɓensa a jihar Kaduna ranar Asabar, yayin da jam’iyyar mai mulki ke ƙara ƙaimi wajen neman goyon bayan al’umma a Arewacin ƙasar.

Tinubu Ya Karɓi Daftarin Kasafin Kuɗin MDD na 2027

Wakilin dindindin na Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce karɓar daftarin kasafin kuɗin ya zama tarihi, yana mai cewa shi ne karo na farko cikin shekaru 66 da shugaban ƙasar ya karɓi irin wannan takarda.

APC Ta Musanta Zargin Shirin Kashe Atiku Abubakar

Jam’iyyar APC ta ce ba ta da hannu a duk wani shiri na cutar da Atiku Abubakar, tare da kira ga Timi Frank da ya miƙa hujjojinsa ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike.

Rahoton ICRC ya nuna ƙaruwar matsalar ƙarancin abinci a Najeriya

Hukumar agaji ta ƙasa da ƙasa, ICRC, ta ce matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ta ƙaru a wasu yankunan arewa maso gabashin Najeriya, inda adadin mutanen da ke fama da ita ya tashi daga kusan 17,000 zuwa 20,000, bisa bayanan da aka tattara daga cibiyoyin lafiya.