Hukumar Jiragen Sama ta Turai ta yi gargaɗi kan zirga-zirgar jiragen sama a yankin Gabas ta Tsakiya
Hukumar Kula da Tsaron Jiragen Sama ta Tarayyar Turai ta fitar da gargaɗi ga kamfanonin jiragen sama kan amfani da sararin samaniyar Bahrain, Kuwait, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da kuma yankunan da ke saman Tekun Oman . Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon ƙaruwar rashin tabbas na tsaro a yankin, wanda ya samo asali daga ci gaba da ayyukan soji da kuma yiwuwar amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa (drones) . A cikin sanarwar, hukumar ta ce akwai yiwuwar jiragen sama su fuskanci barazana idan suka ratsa ta wannan yanki, don haka ta buƙaci kamf
