Harin Bam Ya Kashe Mutum Shida a Damascus na Ƙasar Syria
Aƙalla mutum shida sun mutu, yayin da wasu 22 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a wani gidan shan shayi da ke cike da jama'a a tsakiyar birnin Damascus , babban birnin ƙasar Syria. Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Syria sun ruwaito cewa, bam ɗin ya tashi ne a wani gidan shan shayi da ke gundumar Hejaz , mai nisan kusan mita 100 daga ginin Ma'aikatar Shari'a ta ƙasar. Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Syria ta bayyana cewa an dasa abin fashewar ne a cikin gidan shayin kafin ya tashi, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da jikkata mutane da dama. Har zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki
