Ministan Lafiya na Najeriya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an fitar da matar daga ƙasar ne bisa amincewarsa. Ya ƙara da cewa mijinta, wanda har yanzu bai nuna alamun kamuwa da cutar ba, ya raka ta zuwa Switzerland.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da yake mayar da martani kan wani bidiyo da aka wallafa na yadda aka shigar da matar cikin jirgin sama, ministan ya ce lafiyar matar ta samu sauƙi sosai kafin a kai ta Switzerland.
Sai dai Pate ya jaddada cewa samun sauƙi ba yana nufin matar ta daina iya yaɗa cutar ba. Saboda haka, ya ce ana ci gaba da bin tsauraran matakan kariya da ƙa’idojin lafiyar jama’a domin hana yiwuwar yaɗuwar cutar.
