Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce an gano mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar, lamarin da ya sa aka killace su tare da fara binciken mutanen da suka yi hulɗa da su.
Hukumar ta bayyana cewa an riga an ware mutanen biyu a wuraren kula da masu fama da cututtuka na musamman, yayin da ake ci gaba da tantance waɗanda suka yi mu'amala da su domin gano yiwuwar yaɗuwar cutar.
Haka kuma, NCDC ta ce ana gudanar da gwaje-gwajen ɗakin bincike domin tabbatar da ko mutanen biyu sun kamu da kwayar cutar.
Hukumar ta jaddada cewa har yanzu ana ɗaukar mutanen a matsayin waɗanda ake zargin sun kamu da Ebola, ba tare da tabbatar da kamuwarsu ba. Ta ce sakamakon gwaje-gwaje ne kawai zai tabbatar da hakan.
NCDC ta kuma buƙaci jama'a da su riƙa wanke hannayensu yadda ya kamata, su kula da tsaftar muhalli, tare da bin shawarwarin hukumomin lafiya yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Wannan na zuwa ne bayan da Najeriya ta tabbatar da bullar cutar Ebola a karon farko cikin sama da shekaru goma.
Mutumin da aka fara tabbatar da kamuwarsa da cutar wata mata ce 'yar ƙasar Switzerland mai shekaru 42, wadda ta shigo Najeriya daga Uganda. An tabbatar da cewa ta kamu da nau'in cutar Ebola mai suna Bundibugyo a ranar 20 ga Oktoba.
Daga bisani, an mayar da matar zuwa Switzerland domin ci gaba da samun kulawar lafiya.
