Kamfanin ya ce wannan ci gaba babban mataki ne ga kasuwannin hannayen jari na Afirka, domin tayin ya jawo hankalin masu zuba jari daga nahiyoyi shida na duniya, tare da ba mutane dama su mallaki hannun jari a ɗaya daga cikin manyan masana’antun nahiyar.

A cikin wata sanarwa, Shugaban Kamfanin Dangote Industries Limited, Alhaji Aliko Dangote, ya ce yadda masu zuba jari suka nuna sha’awa ga tayin ya tabbatar da cewa ’yan Afirka suna da muradin zuba kuɗaɗensu a manyan masana’antun da aka kafa a nahiyar.

Dangote ya bayyana cewa wannan sha’awa na nuna yadda masu zuba jari za su iya cin gajiyar ci gaban masana’antu da kuma damar tattalin arziƙin da ke cikin Afirka.

Dangote Ya Yi Bayani Kan Amincewar Masu Zuba Jari

Shi ma Babban Jami’in Gudanarwa na matatar, David Bird, ya ce yadda masu zuba jari daga ƙasashe daban-daban suka amsa tayin ya nuna amincewarsu da girman matatar, ƙwarewarta wajen gudanar da ayyuka da kuma shirye-shiryenta na gaba.

Ya ƙara da cewa samun masu neman zuba jari daga ƙasashe 120 na nuna yadda matatar ta samu karɓuwa a idon masu zuba jari na duniya.

Shirin sayar da hannayen jarin na ba masu zuba jari damar mallakar wani kaso na matatar, yayin da kamfanin ke ƙoƙarin faɗaɗa damar mallakar hannun jari da kuma ƙarfafa rawar da masana’antun Afirka ke takawa a tattalin arziƙin duniya.