Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa jerin sunayen ƴan takarar zaɓen 2027 na ƙarshe, inda ta saka sunan Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

Tun bayan fitar da jerin sunayen farko da hukumar ta yi, rashin ganin sunan Pantami da na Aminu Abdussalam Gwarzo, ɗan takarar gwamna na jam'iyyar NDC a Kano, ya janyo ce-ce-ku-ce, lamarin da ya sa wasu suka miƙa ƙorafe-ƙorafe ga hukumar.

A wancan lokaci, INEC ta bayyana cewa za ta duba ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar mata domin tantance sahihancin bayanan ƴan takarar.

A cikin makon nan ne wasu kafafen yaɗa labarai a Najeriya suka ruwaito cewa hukumar ta kammala nazarin ƙorafe-ƙorafen, inda wasu majiyoyi suka ce an mayar da sunayen ƴan takarar PDP a Gombe da NDC a Kano.

Sai dai wasu rahotannin sun nuna cewa Pantami kaɗai aka mayar da sunansa cikin jerin ƴan takarar.

A sabon jerin da INEC ta wallafa, an ga sunan Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan Gombe na PDP.

Sai dai dangane da takarar Aminu Abdussalam Gwarzo na jam'iyyar NDC a Kano, hukumar ta saka sunan jam'iyyar NDC a jerin, amma ta yi nuni da cewa akwai hukuncin kotu da ya shafi takarar.

Wannan na nuna cewa har yanzu batun takarar ɗan takarar NDC a Kano yana da alaƙa da shari'ar da ke gaban kotu, kuma akwai buƙatar jiran ƙarin bayani kan matsayin ƙarshe na hukumar.