Ƙaramar Ministar Kasafin Kuɗi, Dakta Doris Anite-Uzoka, ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa da Shugaba Tinubu ya jagoranta.

Anite-Uzoka ta ce gwamnati ta fara shirye-shiryen kasafin kuɗin shekarar 2027, kuma tana da niyyar gabatar da shi ga majalisar dokoki kafin ƙarshen shekara.

An Fara Shirye-shiryen Kasafin Kuɗin 2027

Sanarwar ta zo ne makonni kaɗan bayan Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya ya umarci ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati da su gabatar da shawarwarinsu kan kuɗaɗen ma’aikata na shekarar 2027.

Takardar umarnin, mai kwanan wata 4 ga Satumba, 2026, ta samu sa hannun Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi, Tanimu Yakubu.

Takardar ta buƙaci dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati su gabatar da bayanan kuɗaɗen ma’aikatansu, tare da dokokin da suka kafa su.

Sabon Sharadi Kan Hukumomin Gwamnati

Umarnin ya kuma wajabta wa hukumomin gwamnati haɗa takardun dokokin da suka kafa su da shawarwarin kasafin kuɗin ma’aikata da suke gabatarwa.

An bayyana cewa wannan sabon sharadi na da alaƙa da matakan ƙarfafa sa ido da tabbatar da sahihancin hukumomin gwamnati, bayan gano wasu hukumomin bogi da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC) ta yi.

Ana sa ran shirye-shiryen kasafin kuɗin na 2027 za su taimaka wajen tsara kashe kuɗaɗen gwamnati da kuma rabon albarkatun ƙasa ga ma’aikatu da hukumomi a shekarar mai zuwa.

Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken adadin kuɗin da za a ware wa kasafin kuɗin 2027 ko muhimman fannoni da za su fi samun kaso ba.