Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana cewa rikice-rikicen yaƙi da ke gudana tsakanin Isra'ila da Iran, da kuma Rasha da Ukraine, tare da sa hannun Amurka, suna ƙara wahalar da Najeriya da sauran ƙasashe wajen samun kayan aikin soja da ake buƙata domin yaƙar matsalolin tsaro.
Ministan ya kuma nuna damuwarsa kan rashin cikakken kundin bayanan ƙasa (National Database), yana mai cewa hakan na hana hukumomin tsaro, musamman ‘yan sanda, damar bibiyar masu laifi da kuma hana aikata laifuka yadda ya kamata.
Musa ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a taron Nigerian People’s Strategic Conference and Defence Exhibition 2026 da aka gudanar a Abuja.
Da yake magana kan ƙalubalen da ke fuskantar tsarin tsaron ƙasar, ya ce rikice-rikicen duniya sun kawo cikas wajen samun kayan aikin soja, lamarin da ya sa ya zama wajibi Najeriya ta ƙarfafa samar da kayan tsaro a cikin gida.
Yace“Sakamakon yaƙe-yaƙen da ke gudana a Ukraine, Rasha, Iran, Amurka da Isra’ila, samun kayan aiki ya zama abu mai matuƙar wahala. A mafi yawan lokuta, waɗannan ƙasashe suna biyan kuɗi tun da wuri saboda suna da ƙarfin kuɗi, kuma su ne ke samar da yawancin waɗannan kayan. Saboda haka, idan ka je neman saye, tuni sun yi ajiyar kayan domin su, wanda hakan ke sa samun su ya zama da wahala.”.