Rundunar 'Yan Sandan Jihar Zamfara, ta kama mutane 48 da ake zargi da aikata laifuffuka a wani samame da aka kai maboyar masu laifi a cikin birnin Gusau.

A cikin wata sanarwa, Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana cewa aikin, wanda aka gudanar bisa bayanan sirri, ya kuma yi sanadin ƙwato babura 17, kekuna uku, janareta guda ɗaya, lasifikoki uku da ganguna uku, waɗanda ake zargin masu aikata laifuka ne suka yi watsi da su.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan waɗanda aka kama, kuma duk wanda aka samu da hannu a aikata laifi za a gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Zamfara, Ahmad Muhammad Bello, ya sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da yaƙi da aikata laifuka tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'umma a faɗin jihar.