Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) ta amince da sake tsara bashin shirin Project Gazelle na dala biliyan 3.3 ta hanyar sabon shirin samar da kuɗaɗe mai suna Project Gazelle 2, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 4.5.
An cimma wannan matsaya ne a taro na 159 na Majalisar, wanda aka gudanar ta kafar sadarwa ta intanet.
Sabon shirin zai bai wa Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Limited) damar sake tsara ragowar bashin kusan dala biliyan 1.5 da ke ƙarƙashin yarjejeniyar shekarar 2023, tare da samar da ƙarin dala biliyan 3 domin ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen ƙasar na waje da kuma tallafa wa ayyukan gwamnati da bunƙasa ababen more rayuwa.
Majalisar ta amince da shirin ne bayan gabatar da bayanai da suka nuna muhimmancin sa wajen samar da ƙarin kuɗaɗe ga tarayya da kuma wasu fa'idodin tattalin arziki, inda ta yi alƙawarin ba da cikakken goyon baya domin tabbatar da aiwatar da shi.
A yayin taron, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi kira da a samar da manufofin kariyar jin daɗin al'umma masu inganci, masu faɗaɗawa da kuma waɗanda suka dogara da sahihan bayanai domin magance talauci ta fannoni daban-daban a Najeriya.
A cewar Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, an tsara sabon tsarin sake ba da kuɗaɗen ne bisa sharuddan da suka fi sauƙi fiye da na yarjejeniyar farko. Ya ce an rage yawan danyen man da aka jingina daga ganga 90,000 a rana zuwa kusan ganga 78,750 a rana, wanda ke nuna raguwar kashi 12.5 cikin 100.