Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane biyu sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi da sanyin safiyar yau a birnin Damaturu, babban birnin jihar.
An bayyana sunayen waɗanda suka rasu da Isa Haruna mai shekaru 38 da kuma Abba Kyari mai shekaru 18.
A cewar SEMA, lamarin ya faru ne a unguwannin Malam Matari da Pompomari na cikin birnin Damaturu.
Hukumar ta ce tawagarta ta ceto gaggawa, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Yobe, ta gaggauta isa wuraren bayan samun kiran neman agaji.
Sai dai, lokacin da jami'an ceto suka isa wuraren, sun tarar cewa mutanen biyu sun riga sun rasu.
Daga bisani, an kwashe gawawwakin zuwa Sashen Gaggawa da Hadurra (Accident and Emergency Unit) na Asibitin Kwararru na Jihar Yobe da ke Damaturu.
Hukumar SEMA ta yi kira ga mazauna jihar, musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ambaliyar ruwa ke yawan shafa, da su yi taka-tsantsan a lokacin ruwan sama mai ƙarfi, tare da gujewa tsallaka hanyoyi ko magudanan ruwa da ambaliya ta mamaye.