’Yan sanda sun kwance wani bam da ake zargin ’yan bindiga sun binne a yankin Kunchin Kalgo da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.


Hakan na kunshe ne cikin wata samarwa da Jamiʼin Yaɗa Labaran Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar a ranar 13 ga Yuni, 2026.


Sanarwar ta ce jami’an sashen yaƙi da munanan laifuka tare da jami’an sashen kula da abubuwan fashewa sun gano tare da kwance bam din bayan samun sahihan bayanai daga al’umma.


Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna an binne bam din ne domin haddasa asarar rayuka ga matafiya da masu amfani da hanyar.


Rundunar ta yabawa mazauna yankin kan hadin kan da suke bai wa jami’an tsaro wajen samar da bayanan sirri da ke taimakawa wajen dakile ayyukan masu aikata laifuka a fadin jihar.


Sanarwar ta ce, ana ci gaba da kokarin gano tare da cafke wadanda ke da hannu a lamarin, tare da tura jami’an sintiri zuwa yankunan domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.