Hukumar Wayar da Kan Jama'a ta Kasa (NOA) ta bukaci 'yan Najeriya da su rungumi bayar da gudumawar jini domin ceto rayukan mutane da dama


Daraktan hukumar a Jihar Jigawa, Malam Ahmad Tijjani, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi cikin wata sanarwa domin bikin Ranar masu da da Jini ta Duniya ta shekarar 2026.


Ana gudanar da wannan rana a duk ranar 14 ga watan Yuni domin karramawa da yaba wa gudunmawar masu bayar da jini don ceton rai.


Taken bikin na bana shi ne: "Shekaru Ashirin na Bikin Bayar da gudumawar jini, Mun Gode wa Masu Ba da Jini."