Majalisar dokokin Zimbabwe ta amince da ƙudirin doka na tsawaita wa'adin mulkin shugaban ƙasa daga shekara biyar zuwa bakwai. Wannan matakin zai bai wa Shugaba Emmerson Mnangagwa damar ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2030.

Fiye da yan majalisa 200 ne suka kada ƙuri’a don amincewa da daftarin dokar a ranar Alhamis, abin da ya zarce kashi biyu bisa uku da ake buƙata domin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin ƙasar.

Ƙudirin ya kuma soke batun zaɓen shugaban ƙasa kai tsaye, inda daga yanzu ƴan majalisa za su kasance masu zaɓen shugabannin ƙasar.

Mnangagwa, mai shekara 83, ya karɓi mulki ne a shekarar 2017 bayan hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar Robert Mugabe tare da goyon bayan sojoji. Ya kuma ci zaɓe a shekarun 2018 da 2023 da ake takaddama a kansu.

A yanzu ƙudirin ya nufi majalisar dattijawa, inda ake sa ran za a amince da shi kafin shugaban ƙasa ya sanya hannu ya zama doka.