Gwamnatin Tarayyar Najeriya na nazarin wani sabon tsari da zai bai wa ƴan jarida damar yin rakiya da dakarun sojin ƙasar a lokacin da za su ƙaddamar da wasu farmaki na musamman.
Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana hakan a yayin wani taro da Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya a Abuja.
Ministan ya ce matakin zai taimaka wajen inganta yadda ƴan jarida ke bayar da rahotanni kan haƙiƙanin abin da ke faruwa a yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya da sauran matsalolin tsaron cikin gida.
Ya ce hakan zai ƙara fahimtar da jama’a ayyukan da rundunar sojin ƙasar ke yi.
Mai ba shi shawara na musamman, Rear Admiral Olusanya Bankole, wanda ya wakilce shi a wajen taron, ya sanar da cewa Ma’aikatar Tsaro na nazarin yadda za a haɗa ƴan jarida da rundunonin soja yayin wasu ayyuka domin su samu damar bayar da sahihan rahotanni.
"Ma’aikatar Tsaro na nazarin yadda za a haɗa ƴan jarida da rundunonin soja yayin wasu ayyuka domin su samu damar bayar da sahihan rahotanni tare da fahimtar da jama’a haƙiƙanin ayyukan da ake gudanarwa," in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan na daga cikin matakan da ma’aikatar ke ɗauka domin ƙarfafa alaƙa da kafafen yaɗa labarai da kuma tabbatar da cewa bayanan da suka shafi ayyukan soja suna isa ga jama’a cikin sahihanci.