Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah sun amince da tsagaita wuta bayan kwana ɗaya na kazamin faɗa da ya haddasa asarar rayuka da jikkata mutane da dama a Lebanon.
Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar, yayin da kakakin rundunar sojin Isra’ila ya bayyana cewa sojojin ƙasar za su ci gaba da kasancewa cikin shiri idan har bukatar komawa fagen daga ta taso.
Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa cewa ci gaba da rikicin a Lebanon na iya kawo cikas ga ƙoƙarin diflomasiyya da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙoƙarin tabbatarwa tsakanin Amurka da Iran.
A cewar jami’an lafiya na Lebanon, hare-haren da Isra’ila ta kai tun cikin dare sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 47 tare da jikkata kusan mutum 100.
Isra’ila ta ce hare-haren nata martani ne ga kisan sojojinta huɗu da ta zargi mayaƙan Hezbollah da aikatawa.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa tsagaita wutar na iya taimakawa wajen rage tashin hankali a yankin, duk da cewa har yanzu akwai fargabar sake barkewar rikici idan ba a ci gaba da mutunta yarjejeniyar ba.