Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba za ta sake duba sakamakon zabukan fidda gwani da ta gudanar ba, duk da korafe-korafe da bukatun sake zabe daga wasu ‘yan takara da suka fadi. Jam’iyyar ta ce an kammala dukkan matakan sauraron daukaka kara kuma ana shirye-shiryen tura sunayen wadanda suka yi nasara zuwa INEC.


Wani babban jami’in APC ya ce mafi yawan korafe-korafen da aka shigar ba su da karfi, yayin da rahotannin kwamitocin daukaka kara ba su kawo wani babban sauyi ga sakamakon da aka sanar ba. Ya kara da cewa kasa da kashi biyu cikin dari na korafe-korafen ne suka samu nasara.


Sai dai wasu daga cikin ‘yan takarar da ba su gamsu da sakamakon ba sun bayyana fatan cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai shiga tsakani kafin a mika sunayen ‘yan takara ga INEC. Sun yi gargadin cewa rashin warware rikice-rikicen cikin gida na iya yin tasiri ga nasarar jam’iyyar a zaben 2027.