Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada cewa 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta'addanci su miƙa wuya ko kuma su fuskanci cikakken ƙarfin gwamnatin Najeriya.

A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ba za ta amince da buƙatun 'yan ta'adda na sakin waɗanda jami'an tsaro ke tsare da su ba.

Shugaban ya kuma yi gargadin cewa damar da ake bai wa masu aikata laifuffuka ta miƙa wuya ba za ta daɗe ba, yana mai cewa ba za a nuna jinƙai ga waɗanda ke zubar da jinin 'yan Najeriya ba.

Tinubu ya buƙaci 'yan ƙasa su kasance cikin haɗin kai wajen yaƙi da ta'addanci da sauran matsalolin tsaro, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin dawo da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan matsalar tsaro da kuma rasuwar tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar.