Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da hare-haren da take kai wa Lebanon, yana mai cewa lokaci ya yi da za a nuna haƙuri domin kauce wa ƙara rura wutar rikici a yankin.
Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Truth Social, sa’a guda bayan harin da Isra’ila ta kai yankin Dahiyeh da ke Beirut. Ya ce bai kamata harin ya faru ba, musamman a daidai lokacin da ake kusantar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran.
Ya jaddada cewa wajibi ne bangarorin da ke rikicin su nuna takatsantsan, yana mai cewa kamar yadda bai kamata Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon ba, haka ma bai kamata Hezbollah ko wasu ƙungiyoyi su kai hare-hare kan Isra’ila ba.
Sai dai bayan harin, Iran ta yi barazanar dakatar da tattaunawar da take yi da Amurka, yayin da mataimakin shugaban rundunar Khatam al-Anbiya ya bayyana cewa harin ba zai wuce haka ba tare da mayar da martani ba.