Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da cewa ta samu gagarumar nasara a wasu hare-haren da ta kai a sassa daban-daban na ƙasar, inda ta kashe ’yan ta’adda 27 tare da kama mutane 10 da ake zargi da aikata laifuka.

Rundunar ta kuma bayyana cewa sojojinta sun yi nasarar ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, an gudanar da hare-haren ne cikin haɗin gwiwa tsakanin sojojin ƙasa da na sama a jihohin Borno da Plateau da Nasarawa da Akwa Ibom, da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT), bayan samun sahihan bayanan sirri.

Sanarwar ta ce hare-haren sun yi matuƙar dagula ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a yankunan da abin ya shafa.

Rundunar ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar.