Aƙalla mutum 400 ne ake sa ran za a gurfanar a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin kan zargin aikata laifukan ta’addanci, a ɗaya daga cikin manyan shari’o’in ta’addanci da aka taɓa yi a Najeriya.
Shari’ar na nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa ɗaukar alhaki da kuma magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta tsawon shekaru.
Waɗanda ake tuhuma na fuskantar zarge-zarge daban-daban da suka haɗa da kai hare-hare da kuma tallafawa ayyukan ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.
Wannan na zuwa ne bayan wata babbar shari’a da aka gudanar a watan Afrilun 2026, inda aka gurfanar da sama da mutane 500 kan zargin aikata laifukan ta’addanci, kuma aka samu kusan mutum 400 da laifi.
Mahukunta sun ce matakin na da nufin kammala sauran shari’o’in da ke gaban kotu tare da gurfanar da ƙarin waɗanda ake zargi domin fuskantar hukunci idan aka same su da laifi.
Najeriya dai ta shafe fiye da shekaru 16 tana fama da matsalar ta’addanci, wadda ta yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu, yayin da matsalar garkuwa da mutane ke ci gaba da ƙamari a sassa daban-daban na ƙasar.